Karon Farko, Yaron Tinubu Ya Saɓa Masa, Ya Bukaci Janye Afuwa ga Maryam Sanda
- Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa ya soki matakin Bola Tinubu na yin afuwa ga wasu mutane
- Dr. Josef Onoh, ya bukaci shugaban ya janye afuwar da ya bai wa Maryam Sanda da masu laifin miyagun kwayoyi
- Onoh ya ce afuwar ta sabawa adalci da ƙa’ida, tana lalata kimar Najeriya a idon duniya, tare da rage kwarin gwiwar jami’an tsaro
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Bayan afuwar da Bola Tinubu ya yi ga wUs yan Najeriya 175, an fara ce-ce-ku-ce a fadin kasa.
Tsohon hadimin shugaban kasa a yankin Kudu maso Gabas, Dr. Josef Onoh, ya bukaci Bola Tinubu ya sake tunani kan afuwar da ya yi.

Source: Facebook
Rahoton Vanguard ya ce Onoh ya kushe matakin yi wa Maryam Sanda da wasu masu laifin miyagun kwayoyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinunu ya yi afuwa ga mutane 175
Shugaban ya yi afuwa ne ga mutane 175 bisa shawarar kwamitin musamman, ciki har da masu laifin kisa, laifin kwayoyi da kuma wasu baki daga kasashen waje.
Maryam Sanda ta sami hukuncin kisa a shekarar 2020 saboda kashe mijinta, Bilyaminu Bello, yayin wani rikici tsakaninsu.
Afuwa: Na kusa da Tinubu ya ba shi shawara
Onoh ya bayyana matakin a matsayin “mara da’a kuma takewar adalci,” yana mai cewa zai iya lalata martabar gwamnatin Tinubu a idon duniya.
Ya ce bayar da afuwa ga wadanda aka kama da miyagun kwayoyi kamar Nweke Francis Chibueze da Isaac Justina babban kuskure ne da ke bukatar gyara.
Ya ce:
“Duk da cewa doka ta yarda, amma wannan mataki ya saba da gaskiya da adalci, yana cutar da dangin wadanda aka zalunta."
Ya kara da cewa yafewa Maryam Sanda bayan ta janyo “asara ga iyalan Bello” na iya rage darajar rayuwar dan Adam.

Kara karanta wannan
Mansur Sokoto ya yi gugar zana da Tinubu ya yafe wa masu kisan kai da safarar kwaya

Source: Facebook
Gargadin da aka yiwa Tinubu kan afuwa
Onoh ya gargadi cewa yafewa masu fataucin kwayoyi na iya karfafa miyagun dabi’u a cikin al’umma musamman tsakanin matasa.
“Wannan mataki yana nuna cewa fataucin kwayoyi ba laifi ba ne, wanda hakan ke lalata tarbiyyar jama’a."
- Cewar Onoh
Ya kuma ce hakan zai iya bata sunan Najeriya a wajen kungiyoyi kamar UNODC, da rage karfin gwiwar hukumomin tsaro irin su NDLEA da ‘yan sanda.
Ya kara da cewa:
“Wannan yana karyar da tsarin doka, yana rage darajar wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen tabbatar da hukunci."
Daga karshe, ya roki shugaban kasa da ya janye wannan afuwa ta hanyar duba lamarin a fili domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Afuwa : Mansur Sokoto ya soki matakin Tinubu
Kun ji cewa Malamin Musulunci, Farfesa Mansur Sokoto ya bayyana abin da Allah SWT ya yi umarni a kan wadanda ke ketare iyakokin da ya gindaya.

Kara karanta wannan
Maryam Sanda da wasu sanannun mutane 5 da suka shiga cikin wadanda Tinubu ya yi wa afuwa
Ya bayyana haka ne bayan ya ce babu wani 'dan adam ya ke da iko ko hurumin ya yafe laifuffukan da wadansu su ka aikata na shiga hakkin wasu.
Farfesa Mansu ya fadi haka ne bayan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da yafe wa wadanda su ka aikata mugayen laifuffuka a kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
