Maryam Sanda da Wasu Sanannun Mutane 4 da Suka Shiga cikin Wadanda Tinubu Ya Yi Wa Afuwa
Abuja - Maryam Sanda, matar da aka yanke wa hukuncin kisa a 2020 bayan ta kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban PDP na ƙasa, Haliru Bello, na cikin waɗanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lamarin Maryam Sanda ya kasance ɗaya daga cikin fitattun shari’o’in kisan aure da suka fi daukar hankali a tarihin Najeriya.

Source: Facebook
Daily Trust ta tattaro cewa kotu ta same ta da laifin kisa da gangan bayan ta soka wa mijinta wuƙa a lokacin sabani tsakaninsu a gidansu da ke Abuja a watan Nuwamba 2017.
Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa
Bayan doguwar shari’a da ta ja hankalin kasa baki ɗaya, Mai shari’a Yusuf Halilu, a watan Janairun 2020, ya same ta da laifi kuma ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar da mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafin X, Maryam Sanda ta shafe shekara shida da watanni takwas a gidan gyaran hali na Suleja.
Yanzu haka ana sa ran Maryam Sanda za ta sake haɗuwa da ‘ya’yanta biyu da ke zaune tare da danginta tun bayan da aka daure ta.
Sanannun mutane 5 da Tinubu ya yiwa afuwa
Duk da cewa sakin Maryam Sanda shi ne ya fi daukar hankali, ba ita kaɗai ba ce ta ci gajiyar wannan afuwa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Daga cikin mutum 175 da shugaban kasar ya tausaya ya yi wa afuwa akwai:
1. Hon. Farouk Lawan
Farouk Lawal, tsohon ɗan majalisa ne wanda aka same shi da laifin cin hanci a 2021.
Ya riga ya kammala zaman gidan yari, kuma ya shiga cikin mutanen da shugaba Tinubu ya yi masu afuwa.
2. Ken Saro-Wiwa
Shahararren ɗan gwagwarmayar kare muhalli kuma marubuci, na ɗaya daga cikin yan 'Ogoni Nine' da aka kashe a 1995.
Sunansa ya bayyana a cikin jerin sunayen da Shugaba Tinubu ya yi wa afuwa bayan rasuwarsa, abin da ake ganin ya dawo da adalci ga tarihin rayuwarsa.
3. Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa
Soja, wanda aka kama kuma aka kashe a 1986 lokacin rikicin siyasa, shi ma ya samu afuwa bayan rasuwarsa.
Ana ganin dai wannan mataki na yi wa marigayin afuwa na iya zama tamkar wani gyara mai kyau a tarihi.
4. Farfesa Magaji Garba
A shekarun baya-bayan nan aka kama Farfesa Magaji Garba da laifin damfarar kudi ta hanyar amfani da bayanan karya kuma kotu ta daure shi a gidan yari.
Tsohon shugaban jami'ar tarayyar na daya daga cikin mutanen da ke raye da suka shaki iskar yanci bisa karfin ikon shugaban kasa na yin afuwa.

Source: Twitter
5. Sir Herbert Macaulay

Kara karanta wannan
Sanatan APC ya kafa misali da Trump, ya ce da yiwuwar ya zama shugaban Najeriya a 2039
Sir Herbert Macaulay ya kasance shahararren ɗan kishin kasa kuma jarumin dan gwagwarmayar neman ‘yancin Najeriya daga turawan mulkin mallaka.
Turawan mulkin mallaka sun yanke masa hukunci a 1913, amma afuwar da Tinubu ya masa ta dawo masa da hakkin da aka tauye sama da ƙarni guda da ya wuce.
Tinubu ya yi wa mutane 175 afuwa
A wani labarin, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya amince da aiwatar da ikon yafiya na shugaban kasa ga mutane 175 daga sassa daban-daban na kasar nan.
Shugaba Tinubu ya dauki wannan mataki ne bayan MajalisarMagabata ta amince da rahoton Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi (SAN).
Lateef Fagbemi, wanda ya gabatar da jerin sunayen a madadin Tinubu, ya bayyana cewa kwamitin yafiya ne ya hada sunayen wadanda aka yi wa afuwar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

