Babban 'Dan Sanda Ya Yi Wani Irin Mutuwa Mai Rikitarwa a cikin Bandaki
- Wani babban dan sanda mai mukamin ASP a Najeriya yi yi wata irin mutuwa wanda ta tayar da hankula a Mararaba da ke jihar Nasarawa
- An tabbatar da cewa ASP Cyril Takim mai shekaru 54, ya rasu kwatsam bayan ya fadi a ban dakinsa a Mararaba da ke jihar
- Ɗansa Courage Takim Ogar ne ya same shi a sume, inda aka garzaya da shi asibiti, likita daga baya ya tabbatar da mutuwarsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Mararaba, Nasarawa - Mutane sun shiga tashin hankali a Mararaba da ke jihar Nasarawa bayan mutuwar babban jami'in dan sanda.
Majiyoyinmu sun tabbatar da cewa babban jami’in ‘yan sanda mai mukamin ASP, Cyril Takim, ya rasu kwatsam a gidansa wanda ya daga hankulan mutane.

Source: Facebook
Nasarawa: Babban dan sanda ya mutu a bandakinsa
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da haka a shafin X inda ya ce lamarin ya faru a kauyen Aku da ke Mararaba a Jihar Nasarawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce marigayin mai shekaru 54, wanda yake aiki a ofishin mataimakin sufeta-janar na yan sanda a Abuja ya fadi ne a bandaki da misalin ƙarfe 2:50 na rana ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025.
Wani daga cikin iyalansa ya bayyana cewa ɗansa, Courage Takim Ogar, wanda yake da shekara 21, ne ya same shi a sume a bandaki bayan ya shiga ya biya bukata.
Nan take Courage ya garzaya da shi zuwa asibitin kusa da Mararaba domin kokarin ceto lafiyarsa kafin rai ya yi halinsa.
“Lokacin da muka isa asibitin, yana numfashi a hankali, amma daga baya likita ya tabbatar da mutuwarsa."
- Cewar majiyar

Source: Original
Sakamako da yan sanda suka samu bayan bincike
Binciken farko da ‘yan sanda daga sashen Mararaba suka gudanar ya nuna cewa babu wata alama ta tashin hankali ko rauni a jikin marigayin.
Wani jami’in tsaro ya ce an sanya wannan mutuwa cikin rukuni na mutuwar gaggawa ba tare da wata hatsaniya ba kuma an adana gawarsa a dakin ajiyar gawa domin ci gaba da bincike.
Wasu daga cikin abokan aikinsa sun bayyana marigayi Takim a matsayin jami’i mai natsuwa da kwarewa a aikinsa, wanda suka yaba masa saboda jajircewarsa da hakuri.
Rundunar ‘yan sanda a Zone 7, Abuja, har yanzu ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba game da lamarin har zuwa lokacin da tattara wannan rahoton.
An samu gawar shugaban NDLEA a otal
A baya, mun ba ku labarin cewa an shiga fargaba bayan samun gawar shugaban hukumar NDLEA na reshen jihar Cross River a otal wanda ya tayar da hankali.
Majiyoyi sun ce an tsinci gawar Morrison Ogbonna a wani otal da ke Calabar ranar Alhamis 18 ga watan Satumbar 2025 wanda aka rasa dalilin mutuwar saboda lafiyarsa kalau kafin lokacin.
Abokan aikinsa da suka zo daukarsa sun ce sun buga ƙofa sau da yawa ba tare da amsa ba, daga bisani aka same shi matacce wanda daga bisani rundunar yan sanda ta dauke shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

