Sardaunan Zazzau: Tinubu Ya Taya Namadi Sambo Murnar Samun Sarauta
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo murnar samun sarautar Sardaunan Zazzau
- Bola Tinubu ya ce sarautar alama ce ta amincewar masarautar da bajintar Namdi Sambo da sadaukarwarsa wajen cigaban kasa
- Shugaban ya yabawa Sarkin Zazzau saboda ci gaba da girmama mutanen da suka nuna kishin kasa da halin kirki a lokacin da suke aiki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu taya tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo, murnar nada shi Sardaunan Zazzau.
Rahotanni sun nuna cewa Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya shirya bikin nadin sarautar a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, 2025.

Source: Facebook
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wani sako da ya fitar a X.

Kara karanta wannan
Nnamdi Kanu: Tsohon shugaban kasa zai gana da Tinubu kan jagoran 'yan ta'adda a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya bayyana nadin da cewa wata babbar shaida ce ta shugabanci mai kima da namijin ƙoƙarin Namadi Sambo wajen ci gaban ƙasa baki ɗaya.
Tinubu ya taya Namadi Sambo murna
Shugaban ƙasa ya bayyana sarautar Sardaunan Zazzau a matsayin mukami mai cike da tarihi da alaka ta al’adu a Arewacin Najeriya.
Ya ce nadin Namadi Sambo a wannan matsayi ya tabbatar da yadda ya yi fice a fannoni da dama, musamman wajen shugabanci da bayar da gudunmawa ga jama’a.
Tinubu ya ƙara da cewa yabo daga masarautar na da muhimmanci, kasancewar Zazzau ɗaya ce daga cikin tsofaffin masarautu masu daraja a ƙasar Hausa.
Tinubu ya ce Namadi ya yi aiki sosai
A cewar shugaban ƙasa, Namadi Sambo ya kasance mutum mai tawali’u, hazaka, da kishin ƙasa tun lokacin da yake rike da manyan mukaman gwamnati.
The Nation ta rahoto ya ce Namadi ya ba da gudunmawa wajen gina kyakkyawar alaƙa tsakanin gwamnati da al’umma, tare da jajircewa wajen raya ilimi, tsaro da cigaban tattalin arziki.
Tinubu ya ce nadin ba wai yabo ne kawai ga Namadi Sambo ba, ya ce alamar girmamawa ce ga mutanen Zazzau da ke ci gaba da tallafa wa shugabanni masu gaskiya.

Source: Facebook
Namadi: Tinubu ya yabi Sarkin Zazzau
Shugaba Tinubu ya yaba wa Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, bisa ci gaba da bin tsarin girmama mutanen da suka yi fice a fannonin shugabanci da hidima ga jama’a.
Ya ce irin wannan mataki yana ƙarfafa haɗin kai da ƙaunar juna tsakanin shugabanni da al’umma, wanda shi ne ginshiƙin zaman lafiya da ci gaba.
A ƙarshe, Tinubu ya yi kira ga Namadi Sambo da ya ci gaba da zama abin koyi ga matasa, tare da yin aiki tare da shugabannin gargajiya da na addini wajen wanzar da zaman lafiya.
Tinubu ya yi wa masu laifi afuwa
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi wa wasu mutane da aka samu da laifi afuwa.
Rahotanni sun bayyana cewa cikin wadanda aka yi wa afuwa akwai Mamman Vatsa da aka yi wa hukuncin kisa a lokacin Ibrahim Babangida.

Kara karanta wannan
'Babban dalilin da ya sa na zabi Amupitan, shugaban INEC': Tinubu ya fadi hikimarsa
Legit Hausa ta gano cewa shugaban kasar ya sanar da afuwar ne bayan zaman majalisar kolin kasa a fadar Aso Rock Villa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
