Abin Boye Ya Fito: Dalilin da Ya Sa Ministan Tinubu Ya Yi Murabus

Abin Boye Ya Fito: Dalilin da Ya Sa Ministan Tinubu Ya Yi Murabus

  • Tsohon Ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya yi murabus daga mukaminsa bayan an taso shi a gaba kan zargin aikata ba daidai ba
  • Uche Nnaji ya sauka daga mukaminsa ne bayan zargin da aka yi masa na yin amfani da takardun bogi
  • Majiyoyi sun bayyana ainihin dalilin da ya sa tsohon ministan ya hakura da mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sababbin bayanai sun bayyana game da murabus ɗin tsohon Ministan kimiyya da fasaha, Mista Uche Nnaji.

Uche Nnaji ya yi murabus ne daga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bayan an zarge shi da yin amfani da takardun bogi.

Tinubu ya umarci Uche Nnaji ya yi murabus
Shugaban kasa Bola Tinubu da Uche Nnaji. Hoto: @aonanuga1956, @ChiefUcheNnaji
Source: Twitter

Minista ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu

Binciken jaridar The Punch ya gano cewa an umarce shi da ya yi murabus ne bayan zargin yin amfani da takardun bogi.

Kara karanta wannan

'Ba aikin mu ba ne,' Sanata ya fadi masu alhakin tantance takardun ministoci

Ana zargin Uche Nnaji da kirkirar takardar digiri ta BSc da takardar shaidar yi wa kasa hidima ta NYSC.

Ya bayyana cewa ya kammala karatun digirinsa a Jami’ar Najeriya Nsukka (UNN) a shekara ta 1985, amma jami’ar ta karyata wannan ikirari.

Rikicin ya fara ne bayan jaridar Premium Times ta wallafa wani bincike da ya bayyana yadda Nnaji ya mika takardun bogi na digiri da NYSC ga shugaban kasa da majalisar dattawa a lokacin da ake tantance shi a matsayin minista a 2023.

Wane umarni Tinubu ya ba ministan?

Wasu hadiman shugaban kasa sun bayyana cewa Shugaba Tinubu ne ya kira Nnaji zuwa fadar shugaban kasa, inda ya umurce shi da ya yi murabus.

“Shugaban kasa ya gayyace shi zuwa Villa, sannan ya ce ya rubuta takardar murabus. Ba a tilasta masa da barazana ba."
"Ai shugaban kasa ne ya naɗa shi, don haka yana da ikon ya nemi ya sauka daga mukaminsa. Ba shi da wani zaɓi face ya amince."

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya kafa misali da Trump, ya ce da yiwuwar ya zama shugaban Najeriya a 2039

- Wata majiya

Wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa Nnaji ba ya da wani zaɓi illa ya yi murabus, domin zargin ya zama abin kunya ga gwamnati.

“Shugaban kasa ya bukace shi ya yi murabus. Ya zama abin kunya ga gwamnati, kuma idan aka ci gaba da jan lokaci, abin zai kara lalacewa."
"Wasu ministoci da mataimakan shugaban ƙasa sun ba da shawarar cewa ya fi kyau a sallame shi da wuri. Zargin ba abin da za a iya kyalewa ba ne."

- Wata majiya

Uche Nnaji ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu
Tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji. Hoto: @ChiefUcheNnaji
Source: Twitter

Da aka tambayi ko shugaban kasa zai ɗauki mataki kan hukumar DSS saboda rashin gano takardunsa na bogi ne tun kafin a amince da shi, sai majiyar ta ce:

“Ba za a ɗora laifin gaba ɗaya kan DSS ba. Me za a ce game da majalisar dattawa da ta tantance shi? Su ma suna da alhakin binciken takardun da aka gabatar.”

Tinubu ya yi afuwa ga wasu 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Kano: 'Dan jarida ya debo ruwan dafa kansa, ICPC ta kama shi kan zambar N14m

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi afuwa ga wasu 'yan Najeriya 175 da aka yankewa hukunci daban-daban.

Hakazalika shugaban kasan ya yi sassauci ga wasu mutanen da ke tsare a gidan gyaran hali.

Daga cikin mutanen da Shugaba Tinubu ya yi wa afuwa har da tsohon ministan birnin Abuja, Manjo Janar Mamman Vatsa (mai ritaya).

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng