Kwana Ya Kare: Abokin Atiku Abubakar kuma Babban Dan Siyasa a Najeriya Ya Rasu

Kwana Ya Kare: Abokin Atiku Abubakar kuma Babban Dan Siyasa a Najeriya Ya Rasu

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya sanar da rasuwar abokinsa tun na yarinta, Yakubu Tsala
  • Atiku ya bayyana alhini da jimamin rasuwar Yakubu, Shettima Mubi wanda ya ce sun hadu tun yana makarantar sakandire
  • Marigayin ya kasance abokin siyasar shi kuma ya rike mukamai daban-daban na gwamnati kafin ya koma harkar sadarwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Adamawa - Abokin tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, wanda suka yi kuruciya tare, Yakubu Tsala ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayi Yakubu Tsala, wande shi ne Shettima Mubi, ya kuma kasance abokin siyasa ga Atiku Abubakar na tsawon lokaci, har zuwa rasuwarsa.

Alhaji Atiku Abubakar.
Hoton tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar. Hoto: @Atiku
Source: Facebook

Atiku ya sanar da rasuwar abokinsa

Atiku ya tabbatar da rasuwar dattijon kuma dan siyasa a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, 9 ga watan Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna na shirin komawa APC, tsohon jagora a Majalisar Dattawa ya fice daga PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan siyasar ya bayyana alhini da bakin ciki kan rasuwar abokin da suka yi ƙuruciya, kuma abokinsa na siyasa na dogon lokaci, Yakubu Tsala.

Tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP ya ce sun fara abota tun lokacin da marigayin yake karatu a makarantar sakandire ta gwamnati da ke garin Ganye.

“Zuciyata ta karye da na samu labarin rasuwar abokina tun ina yaro kuma abokin siyasa na dogon lokaci, Yakubu Tsala (Shetima Mubi),” in ji Atiku.

Wuraren da Yakubu Tsala ya yi aiki

Ya ce marigayin ya yi kyakkyawan aiki wajen hidimar jama’a, yana mai bayyana cewa ya rike mukamai da dama a ƙasar nan.

Atiku ya ambaci wasu daga cikin mukaman da marigayin ya rike ciki har da Shugaban Lake Chad Research Institute da kuma Daraktan Hukumar Kula da Iyakokin Najeriya.

Bayan ya kammala aikinsa na gwamnati, Atiku ya bayyana cewa Ykubu Tsala ya shiga harkar kasuwanci, musamman a fannin harkokin sadarwa.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa da aka ja kunnensu kan yin takara a 2027

A nan ne aka nada shi a kwamitin gudanarwa na tashar Gotel TV da Radio, mallakar Atiku Abubakar, domin amfani da ƙwarewarsa.

Atiku da Marigayi Yakubu Tsala.
Hoton Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar tare da Marigayi Yakubu Tsala. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Wazirin Adamawa ya yi ta'aziyyar Yakubu

Atlku ya kuma yi wa marigayin addu'ar Allah gafarta masa kuma Ya bai wa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi da suka yi.

“Ina roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya ba iyalansa, abokansa da duk masu jimamin rasuwarsa haƙuri da juriya.
"Allah Ya ji kan sa Ya ba shi hutu na har abada. Sai mun sake haduwa, Yakubu. Marigayi Yakubu Tsala ya bar babban gado na sadaukarwa, aminci da jajircewa ga ci gaban ƙasa, in ji Atiku.

Dattijon kasa kuma tsohon jakada ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa tsohon jakadan Najeriya a kasar Birtaniya, Christopher Kolade ya rasu yana da shekaru 92 a ranar Laraba 8 ga watan Oktoba, 2025.

An haifi Kolade a ranar 28 ga Disamba, 1932 a Erin-Oke, Jihar Osun, mahaifinsa malamin coci ne na Anglican, ya yi karatu a kwalejin gwamnati da ke Ibadan.

Kara karanta wannan

Wasu daga cikin mutane 175 da Tinubu ya yi wa afuwa da laifin da suka aikata

Maeigayin ya yi aiki a matsayin jakadan Najeriya a Birtaniya, inda ya ba da gagarumar gudummawa, ya yi tabbatar da gaskiya da mutunci a tsarin diflomasiyya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262