'Kowa zai Yi Muhalli,' Gwamnatin Tinubu za Ta Samar da Gidaje Masu Araha

'Kowa zai Yi Muhalli,' Gwamnatin Tinubu za Ta Samar da Gidaje Masu Araha

  • Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na samar da gidaje masu saukin farashi domin tallafawa ‘yan kasa masu karamin karfi
  • Ministan gidaje da raya birane, Ahmed Dangiwa, ya ce ana tsara sabon tsarin kudi domin jama’a su mallaki gida cikin sauki
  • Ya kara da cewa ce gwamnati za ta kafa cibiyoyin kera kayan gini a yankuna shida na kasar domin rage dogaro da kasashen ketare

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu– Ministan gidaje da raya birane, Ahmed Dangiwa, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana aiwatar da matakai daban-daban domin samar da gidaje masu saukin farashi.

Ahmed Dangiwa ya bayyana cewa shirin zai amfani ‘yan kasa masu karamin karfi domin su samu damar mallakar muhalli.

Ministan gidaje, Ahmed Dangiwa
Ministan gidaje, Ahmed Dangiwa na wani bayani. Hoto: @Arch_Dangiwa
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa Dangiwa ya bayyana haka ne yayin wani taro da aka gudanar a ranar Alhamis a Enugu.

Kara karanta wannan

Hijabi: Zulum ya dauki mataki kan zargin cin zarafin mata musulmai a asibitocin Borno

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ma’aikatarsa tana amfani da tsarin samar da gidaje wajen samar da tsarin kudi na musamman domin tabbatar da cewa 'yan kasa sun mallaki muhalli.

Tsarin samar da gidaje masu araha

Ministan ya bayyana cewa gwamnati za ta rika sayar da gidajen ne bisa tsarin da bai wuce kashi 1 bisa 3 na kudin shigan mutum ba.

Dangiwa ya bayyana cewa za a yi haka ne domin tabbatar da cewa mallakar gida ya zama abu mai yiwuwa ga kowa.

Ya ce, wannan tsari zai taimaka wajen rage gibin da ke tsakanin masu kudi da marasa shi, tare da baiwa kowane dan kasa damar rayuwa cikin kwanciyar hankali.

Za a kafa cibiyoyin kera kayan gini

Dangiwa ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya tana shirin kafa cibiyoyin kera kayan gine-gine a kowanne yanki na kasar.

Hakan, a cewarsa, zai taimaka wajen daidaita da farashin kayayyaki, samar da ayyukan yi da rage dogaro da shigo da kayan gini daga kasashen waje.

Kara karanta wannan

Triumph: Sheikh Gumi ya kawo mafita kan rikicin Kano, ya yi kira ga Abba Kabir

Ministan ya ce:

“Wadannan cibiyoyi za su zama wata hanya ta tabbatar da cewa gidajen mu na ‘Made in Nigeria’ ne, alamar cigaban tattalin arzikin mu.”
Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a wani taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Mallakar gida: Za a yi hadaka da jihohi

Ministan ya bayyana cewa gwamnati ta hada kai da shirin Know This Nigeria Network domin cigabda da tallata shirinta na bude hanyoyin mallakar gidaje.

Ya ce, wannan shiri zai hada karfi da karfe tsakanin Gwamnatin Tarayya da jihohi wajen bude kofar mallakar gida ga jama’a a fadin Najeriya.

Vanguard ta wallafa cewa Dangiwa ya bayyana cewa za a fara shirin ne a jihar Katsina daga karshen wannan wata kafin ya kai zuwa sauran jihohi.

Fadar shugaban kasa ta kare Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta kare gwamnatin Bola Tinubu kan cewa an samu karuwar talakawa duk da tsare tsarensa.

Hakan na zuwa ne bayan bankin duniya ya ce an samu karin mutane sama da miliyan 130 da suke cikin talauci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kano: 'Dan jarida ya debo ruwan dafa kansa, ICPC ta kama shi kan zambar N14m

Hadimin shugaban kasa, Sunday Dare ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar bayan bankin duniya ya fitar da rahotonsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng