Shugaba Bola Tinubu Ya Yi Afuwa ga Wasu 'Yan Najeriya 175

Shugaba Bola Tinubu Ya Yi Afuwa ga Wasu 'Yan Najeriya 175

  • Wasu 'yan Najeriya da aka yankewa hukunci sun samu afuwa daga wajen Shugaban kasa, Mai girma Bola Ahmed Tinubu
  • Tinubu ya amince da afuwar ne yayin taron majalisar koli da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja
  • Daga cikin mutanen da aka yi wa afuwa har da sanannen dan kishin kasa, marigayi Herbert Macauley

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da aiwatar da ikon yafiya na shugaban kasa ga mutane 175 daga sassa daban-daban.

Daga cikin mutanen da Shugaba Tinubu ya yi wa afuwar har da fitaccen dan kishin kasa, Herbert Macaulay, da tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, Manjo Janar Mamman Vatsa (mai ritaya).

Shugaba Tinubu ya yi wa wasu 'yan Najeriya afuwa
Shugaban kasan Najeriya, Mai girma Bola Tinubu. @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce an tabbatar da afuwar ne a ranar Alhamis, yayin taron majalisar koli ta kasa da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan

Majalisa ta cin ma matsaya kan zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya

An amince da afuwar da Tinubu ya yi

Amincewar ta zo ne bayan majalisar koli ta amince da takardar da babban lauyan gwamnati kuma Ministan shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) ya gabatar yayin taron da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Lateef Fagbemi, wanda ya gabatar da jerin sunayen a madadin shugaban kasa, ya bayyana cewa an samo sunayen ne daga rahoton kwamiti na musamman kan ikon yafiya, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da labarin.

Kwamitin ya duba bukatun afuwa da sassauci bisa tanadin kundin tsarin mulki.

Kodayake ba a fitar da cikakken jerin sunayen waɗanda abin ya shafa ba, majiyoyi daga taron sun tabbatar da cewa fitattun mutane irin su Herbert Macaulay da Mamman Vatsa na cikin waɗanda aka yi wa afuwa.

Herbert Macaulay, wanda sanannen dan kishin kasa ne, an taba yanke masa hukunci har sau biyu a lokacin mulkin mallaka na Turawan Birtaniya a Legas.

Kara karanta wannan

IBB, Abdulsalami sun halarci taron majalisar koli, karon farko babu Buhari

Daga cikin mutane 175 da aka yafewa, mutane 82 sun samu cikakkiyar afuwa, 65 an rage musu hukunci, yayin da hukuncin kisa na mutane bakwai aka mayar da shi zuwa daurin rai da rai.

Sauran wadanda aka yafe masu laifinsu sun hada da tsohon 'dan majalisa Farouq Lawan da aka da laifi wajen binciken badakalar tallafin man fetur.

'Yan gwagwarmayar yankin Ogoni Ken Saro-Wiwa, Saturday Dobee, Nordu Eawo, Daniel Gbooko, Paul Levera, Felix Nuate, Baribor Bera, Barinem Kiobel da John Kpuine sun samu shiga.

Daily Trust ta ce an kuma karrama Albert Badey, Edward Kobani, Samuel Orage da Theophilus Orage bayan sun rasu.

Uba Sani ya yabawa Tinubu

Gwamna Uba Sani ya tabbatar da afuwar da shugaban kasa ya yi ga mutanen.

Yayin da zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, Gwamna Uba Sani, ya yabawa Shugaba Tinubu kan afuwar da ya yi musu.

Gwamna Uba Sani ya yabawa Shugaba Tinubu
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani. Hoto: @ubasanius
Source: Facebook
“Mutane 82 sun samu cikakkiyar afuwa, 65 an rage musu hukunci, yayin da aka mayar da hukuncin kisa na bakwai zuwa daurin rai da rai."
"Wannan mataki ya nuna jajircewar shugaban kasa wajen tabbatar da adalci da kawo gyara a tsarin gidajen gyara hali.”

Kara karanta wannan

Sallama da murabus: Jerin ministoci 9 da aka rasa a gwamnatin Bola Tinubu

- Gwamna Uba Sani

Shugaba Tinubu ya nada sabon shugaban INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Shugaba Tinubu ya nada Farfesa Joash Amupitan a matsayin wanda zai maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu.

Mai girma Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Farfesa Amupitan shi ne mutum na farko daga jihar Kogi a yankin Arewa ta Tsakiya da aka zaɓa don rike mukamin shugabancin INEC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng