An Kai Kungiyoyin SSANU da NASU Wuya, Sun Barke da Zanga Zanga a Abuja

An Kai Kungiyoyin SSANU da NASU Wuya, Sun Barke da Zanga Zanga a Abuja

  • Ma'aikatan Jami'o'i da na Kwalejojin Ilimi na Tarayya sun fara zanga-zanga a fadin Najeriya yau Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025
  • Masu zanga-zangar karkashin kungiyoyin SSANU da NASU sun nuna damuwa kan yadda gwamnati ta yi biris da koke-kokensu
  • Sun lissafo batutuwa shida da suke neman gwamnatin tarayya ta ta cika masu kamar yadda ta yi alkawari a baya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon.shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ma'aikatan Jami'o'in Najeriya da Kwalejoji sun barke da zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja yau Alhamis, 9 ga watan Oktoba, 2025.

Kungiyar Ma'aikatan Jami'o'i (SSANU) da takwararta ta ma'aikatan Kwalejojin Najeriya (SANU) sun fara zanga-zanga ne saboda rashin cika alkawarin gwamnatin tarayya.

Zanga zangar SSANU da NASU.
Hoton wasu daga cikin mambobin NASU da SSANU da suka fito zanga-zanga a Abuja. Hoto: @SSANU
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta tattaro cewa zanga-zangar na gudana a Jami'ar Yakubu Gowon (wacce aka fi sani da Jami'ar Abuja a baya) da sauran Jami'o'i a fadin kasa.

Kara karanta wannan

Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SSANU da NASU sun fara zanga-zanga

A Abuja, shugabannin zanga-zangar sun haɗa da Kwamared Nurudeen Yusuf, shugaban SSANU na Jami’ar Yakubu Gowon, da Kwamared Sadiya Ibrahim Hassan, shugabar NASU ta jami’ar.

Kungiyoyin sun zargi gwamnatin tarayya da rashin cika alkawari, sakaci da karya yarjejeniyoyin hadin gwiwa da aka cimma tsakaninsu tun shekarar 2022.

Da yake jawabi ga manema labarai, Kwamared Yusuf ya ce sun shiga zanga-zangar ne bayan koke-koke, gargadi da wa’adin da suka ba gwamnati amma ta yi kunnen uwar shegu da su.

Abubuwa 6 da kungiyoyin suke nema

Kungiyoyin sun bayyana batutuwa guda shida da gwamnati ta gaza warware wa wanda suka haifar da wannan zanga-zanga, da suka haɗa da:

1. Rashin sabunta yarjejeniyar 2009 FGN/NASU/SSANU,

2. Rashin biyan karin albashi na kashi 25% da 35% da aka amince da su

3. Raba kudin alawus na Naira biliyan 50 ba bisa adalci ba

4. Rashin biyan albashin watanni biyu da aka rike wa ma'aikatan a 2022

Kara karanta wannan

Ma'aikatan jami'o'i sun fusata da Tinubu, za su rufe titunan Najeriya a ranar Alhamis

5. Rashin biyan kudaden da ake cire wa ga wasu mambobin NASU, SSANU

6. Da kuma rashin kula da walwalar ma’aikatan da ba malamai ba a jami’o’i.

Kungiyoyin ma'aikatan Jami'o'i da Kwalejojin Ilimi.
Hoton tanbarin kungiyoyin SSANU da NASU. HOTO: SSANI, NASU
Source: Twitter

Asalin matsalar gwamnati da SSANU, NASU

Sun bayyana cewa wannan matsalar ta samo asali ne tun daga rashin sabunta yarjejeniyar 2009, wacce ya kamata a dinga duba ta duk bayan shekaru uku.

Sun ce tun daga 2012 an kafa kwamitoci da dama, amma babu wani sakamako na zahiri da aka samu, in ji rahoton Tribune Nogeria.

Shugabar NASU, Kwamared Sadiya Hassan, ta ce goyon bayan kafa kwamitoci maimakon aiwatar da abubuwan da aka riga aka cimma ya ƙara lalata alakar tsakanin gwamnati da kungiyoyin.

Gwamnatin Tarayya ta fara rokon ASUU

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta roƙi ƙungiyar malaman jami’o'i ta kasa (ASUU) da ta janye shirinta na fara yajin aikin gargadi.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ne ya yi wannan roko a taron manema labarai a Abuja, ya tabbatar wa ASUU cewa za a biyaa mata bukatunta sannu a hankali.

Kara karanta wannan

Amupitan: Farfesa daga jami'ar Jos na dab da zama sabon shugaban hukumar INEC

Alausa ya ce gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da matakan sulhu da ƙungiyar domin a taka wa yajin aiki burki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262