Najeriya ta Karyata Bankin Duniya kan Samun Talakawa Miliyan 139 a Mulkin Tinubu

Najeriya ta Karyata Bankin Duniya kan Samun Talakawa Miliyan 139 a Mulkin Tinubu

  • Fadar Shugaban Kasa ta ce alkaluman Bankin Duniya da suka nuna cewa mutane miliyan 139 a Najeriya na fama da talauci ba gaskiya ba ne
  • Mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan yada labarai, Sunday Dare, ya bayyana cewa rahoton ya dogara ne da bayanan tsohuwar kididdiga
  • Dare ya ce Najeriya na kan tafarkin farfadowa da shirya gyare-gyaren da za su inganta tattalin arziki da walwalar ‘yan kasa a nan gaba kadan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Fadar Shugaban Kasa ta musanta rahoton Bankin Duniya da ya ce kusan kashi 60 cikin 100 na ‘yan Najeriya, wato mutum miliyan 139, na rayuwa cikin talauci.

Mai bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan yada labarai, Sunday Dare ne ya bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Akpabio ya yi maganar farko bayan bude majalisa da dawowar Sanata Natasha

Sunday Dare, Bola Tinubu
Hoton Shugaba Tinubu da Sunday Dare. Hoto: Bayo Onanuga|Sunday Dare
Source: Twitter

Legit Hausa ta gano cewa Sunday Dare ya bayyana haka ne a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X.

Magana fadar shugaban kasa kan talauci

Fadar Shugaban Kasa ta ce kididdigar Bankin Duniya ta dogara ne da tsarin PPP, wanda idan aka juyar da shi zuwa Naira, ya kai kusan N100,000 a wata, sama da mafi karancin albashi na N70,000.

A cewar Dare, hakan na nuna cewa kididdigar ba ta nuna ainihin yadda talaucin yake a Najeriya ba, domin yawancin jama’a suna dogaro da tattalin arzikin da ba ya cikin bayanan PPP.

Ya ce gwamnati na kallon rahoton a matsayin wanda bai nuna hakikanin yadda ake rayuwa a shekarar 2025 ba.

Gwamnati ta ce tattalin arziki na farfadowa

Sunday Dare ya bayyana cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne canjin da ake samu, ba lambar alkaluma ba.

Punch ta wallafa cewa ya ce tattalin arzikin Najeriya a yanzu na kan tafarkin farfadowa bisa tsarin da ke samar da cigaban da ya shafi kowa da kowa.

Kara karanta wannan

Tsohon hafsan tsaro ya fadi babban kalubalen da ya fuskanta a mulkin Buhari

Hadimin shugaba Tinubu, Sunday Dare
Sunday Dare da ya kare gwamnatin Tinubu kan rahoton bankin duniya. Hoto: Sunday Dare
Source: UGC

Ya ce gwamnatin Tinubu ta ƙara yawan shirye-shiryen tallafi da jin kai domin rage radadin sauye-sauyen da aka yi, tare da shimfiɗa tubalin cigaba.

Cikin shirye-shiryen da ya ambata akwai shirin tallafin kuɗi na gaggawa, wanda ya kai ga gidaje miliyan 15.

Gwamnati ta ce ana magance talauci

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa gwamnati tana magance tushen matsalolin tattalin arziki da suka hana cigaba, kamar cire tallafin man fetur, haɗa tsarin musayar kuɗi.

Rahoton ya kara da cewa ma’aikatan Bankin Duniya ma sun amince cewa wadannan sauye-sauyen suna kawo cigaba ga tattalin arzikin ƙasa.

Dare ya ce burin gwamnatin Tinubu shi ne tabbatar da cewa farfadowar tattalin arziki ya zama abin da jama’a ke iya amfana ta fuskar farashin abinci, samar da ayyuka, da sauransu.

An yi taron tattalin arziki a jihar Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Bauchi ta shirya taron tattalin arziki na kwana biyu da ya shafi jawo masu zuba jari.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ADC ta sake taso Shugaba Tinubu a gaba kan rashin tsaro

Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa yanzu ne lokaci mafi dacewa da masu zuba jari za su shigo Najeriya.

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, mai Alfarma Sarkin Musulmi, gwamna Babagana Umara Zulum sun halarci taron.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng