An Wanke Ganduje da Iyalansa kan Batun Karkatar da Biliyoyi a Tashar Tsandaurin Dala

An Wanke Ganduje da Iyalansa kan Batun Karkatar da Biliyoyi a Tashar Tsandaurin Dala

  • Tashar tsandaurin Dala ta bayyana cewa babu wani ɗan gidan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, da ke da hannun jari a cikinta
  • Sakataren tashar, Adamu Sanda, ya ce rahotannin da ake yadawa kan mallakar ‘ya’yan Ganduje ba gaskiya ne kuma siyasa ce ta haddasa su
  • Tashar ta bayyana cewa babu wani lokaci a baya da gwamnatin Kano ta mallaki kaso a cikinta ko ta samu wakilci a hukumar gudanarwata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Tashar tsandaurin Dala ta musanta rahotannin da ke yawo a intanet cewa ‘ya’yan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, suna daga cikin masu hannun jari.

Sakataren tashar, Adamu Sanda, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya, mai cike da ruɗani da kuma abin da aka ƙulla da niyyar siyasa.

Kara karanta wannan

Kano: 'Dan jarida ya debo ruwan dafa kansa, ICPC ta kama shi kan zambar N14m

Abdullahi Umar Ganduje
Tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa ya ce babu wani lokaci da iyalan Ganduje ko gwamnatin Kano suka mallaki kaso ko suka shiga harkokin gudanarwa a tashar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, bincike daga CAC da kuma takardun hukumar gudanarwa sun tabbatar da cewa babu wanda ya taɓa baiwa iyalan Ganduje wani kaso ko mukami a tashar tsandaurin.

An wanke Ganduje da iyalansa daga zargi

Sanda ya ce tashar ta ga ya dace ta fito da wannan bayani ne saboda yaduwar wani rahoto da ke cewa ‘ya’yan Ganduje sun mallaki wani kaso na hannun jari a tashar tsandaurin.

Ya bayyana cewa takardar ta bogi ce, kuma an rubuta ta ne ba tare da amincewar sauran shugabanni ba.

Ya ƙara da cewa babu wata shaida daga CAC ko wata hujja ta doka da ke nuna an baiwa ‘ya’yan Ganduje wani kaso.

Wane ne ya mallaki tashar tsandaurin Dala?

Sanda ya ce tashar tun asali mallakar Ahmad Rabi’u da abokan aikinsa ne, kafin daga baya ya gayyaci kamfanin City Green Enterprises (CGE) domin saka hannun jari.

Kara karanta wannan

Ecuador: Matasa kusan 500 sun rufe shugaban kasa da jifa da duwatsu

A cewar sa, CGE ya saye kaso 80 na hannun jari a tashar, yayin da Ahmad Rabi’u ya riƙe kaso 20 wanda ma bai kammala biyan sa ba.

TAshar tsandaurin Dala a Kano
Tashar tsandaurin Dala da ake magana a kanta. Hoto: Kano Chronicle
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa Sanda ya kara da cewa ba a taba shigar da gwamnatin Kano ko iyalan Ganduje cikin cinikin ba.

Gwamnatin Kano ba ta da kaso

Tashar ta kuma karyata ikirarin da ke cewa gwamnatin Kano tana da kaso 20 a cikinta ko tana da wakili a hukumar gudanarwarta.

Sanda ya bayyana cewa duk hulɗar gwamnati da tashar ta ta’allaka ne da tallafin aikin CSR da ta bayar bisa roƙon hukumar NSC domin farfaɗo da aikin tashar jirgin ƙasa.

Ya ƙara da cewa irin wannan tallafi na gine-gine da kayayyakin more rayuwa ba yana nufin mallakar kaso ba ne, domin ya fi dacewa da taimako don cigaban kasuwanci da sufuri a jihar.

An fara binciken Ganduje a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta fara sabon bincike kan tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Rahotanni sun bayyana cewa za a yi binciken ne kan zargin karkatar da wasu makudan kudi da aka ce an yi a zamaninsa.

Kara karanta wannan

Ganduje: Mamallaka tashar tsandauri sun fito da bayanai a kan gwamnatin Kano

Binciken na cikin matakan da gwamnatin Kano, karkashin Abba Kabir ke dauka domin yaki da cin hanci da rashawa a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng