Abin da Mahmood Yakubu ya Fadawa Tinubu a Takardar Ajiye Shugabancin INEC
- Mahmood Yakubu ya miƙa wa shugaban ƙasa Bola Tinubu takardar ajiye aikinsa a hukumance ranar 3, Oktoba, 2025
- Ya roƙi a amince da murabus ɗinsa daga ranar Talata, 7, Oktoba, kafin karewar wa’adin aikinsa a watan Nuwamba
- May Agbamuche-Mbu ce ta karɓi ragamar shugabancin hukumar zabe ta INEC a matsayin mai rikon kwarya a halin yanzu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Bayan shekaru 10 yana jagorantar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya ajiye aikinsa daga mukamin shugaban hukumar.
Rahotanni sun nuna cewa hakan na zuwa ne kusan wata guda kafin karewar wa’adin aikinsa na biyu a hukumance.

Source: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa bayan fara jagorantar hukumar a shekarar 2015, ya samu karin wa’adi a 2020 domin ci gaba da jagoranci na shekaru biyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa shugaban ƙasar ya amince da murabus ɗin Mahmood Yakubu, tare da godiya bisa rawar da ya taka wajen tabbatar da gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.
Me Mahmood Yakubu ya fada wa Tinubu?
A cewar bayanan da suka fito daga fadar shugaban ƙasa, Farfesa Yakubu ya ajiye aikinsa ne domin guje wa tsawaita zamansa har zuwa zaɓen gwamnan jihar Anambra.
Hukumar INEC ta sanar da cewa ta tsara gudanar da zaben Anambra ne a ranar 8, Nuwamba, 2025.
A cikin wasikar da ya rubuta wa shugaban ƙasa Tinubu, Yakubu ya bayyana godiyarsa bisa damar da aka ba shi ta yin hidima ga ƙasa.
Ya roƙi a amince da murabus ɗinsa daga ranar 7, Oktoba, 2025, kafin karewar wa’adinsa a ranar 9, Nuwamba.
Mahmood Yakubu ya bayyana wa Tinubu cewa:
'Ina godiya bisa damar shugabantar hukumar zabe da aka bani."

Source: Twitter
Martanin Tinubu ga Mahmood Yakubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus ɗin shugaban INEC ɗin tare da gode masa saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen gina tsarin dimokuraɗiyya.
Legit ta gano haka ne a wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya wallafa a X a ranar Talata.
Onanuga ya ce shugaban ƙasa ya yaba masa bisa gudanar da zaɓuka masu inganci da suka taimaka wajen tabbatar da dimokuraɗiyya a ƙasar.
May Agbamuche-Mbu ta karɓi ragama
A yayin taron da aka gudanar a hedikwatar hukumar INEC a Abuja, Yakubu ya mika ragamar shugabanci ga May Agbamuche-Mbu.
A yanzu haka ita ce za ta jagoranci hukumar a matsayin mai rikon kwarya har sai an nada sabon shugaban dindindin.
Majalisar Koli ta Ƙasa za ta gana ranar Alhamis, 9, Oktoba, 2025, domin tattauna jerin sunayen wadanda za su maye gurbin Mahmood Yakubu.
Ana sa ran tsofaffin shugabanni Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, da gwamnonin jihohi za su bayar da shawara ga shugaban ƙasa kan wanda zai dace da wannan mukami.
Legit ta tattauna da Hamza
Wani tsohon ma'aikacin INEC na wucin gadi, Hamza Adamu ya bayyana cewa za a iya cewa Mahmood Yakubu ya yi kokari.
Ya ce:
"A lokacin da muka yi aiki 2023, har ga Allah an umarce mu da muyi aiki bisa gaskiya kuma ba mu yi magudi ba. A kan haka zan iya cewa ya yi kokari.
"Ina fatan wanda zai gaje shi ya kasance ya fi shi kokari."
Bayani kan shugabar rikon INEC
A wani rahoton, kun ji cewa Legit ta tattaro bayanai masu muhimmanci kan shugabar rikon kwarya ta hukumar INEC, May Agbamuche-Mbu.
Binciken Legit Hausa ya gano cewa an haifi May Agbamuche-Mbu a jihar Kano kuma a nan ta fara karatu.
Sabuwar shugabar rikon kwaryar ta yi karatun lauya kuma ta rike mukamai daban daban a ciki da wajen Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


