Tinubu Ya Kunyata Majalisar Tarayya, Ya Ki Sanya Hannu kan Wasu Sababbin Kudirori 2
- Shugaba Bola Tinubu ya ki amince da wasu kudurorin dokoki biyu da majalisar tarayya ta gabatar masa bayan tantance su
- Kudurorin sun hada da gyaran dokar cibiyar fasahar zirga-zirga ta Najeriya da dokar kafa asusun dakin karatu na kasa, 2025
- Shugaban kasar ya bayyana cewa dokokin na dauke da tanade-tanade a suka saba da manufofin kudi da haraji na gwamnati
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ki sanya hannu kan kudurorin doka biyu da majalisar tarayya ta amince da su kwanan nan.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa cewa kudurorin dokar biyu suna dauke da kurakurai da sabani da tsarin tattalin arziki da dokokin gwamnati.

Source: Twitter
Tinubu ya ki sanya hannu kan dokoki 2
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa kudurorin dokokin da Tinubu ya ki sanya wa hannu su ne:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Kudurin dokar cibiyar fasahar sufuri ta Najeriya (da aka sabunta)
- Kudurin dokar kafa asusun dakin karatu na kasa (NLTF) 2025.
Tinubu ya bayyana matsayinsa ne a wasiku daban-daban da ya aika wa majalisar dattawa, wanda Sanata Godswill Akpabio, ya karanta yayin zaman majalisar a ranar Talata.
Dalilan Tinubu ya ki amincewa da dokokin
A cikin wasikar farko, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa kudurin gyaran dokar cibiyar sufuri ta ba cibiyar izinin karbar 1% daga dukkan kudaden shiga da fita na kaya a tashoshi, wanda ya ce “ba adalci ba ne ga ‘yan kasuwa kuma ya saba da manufar gwamnati ta rage haraji.”
Haka kuma, dokar ta ba cibiyar ikon karbar rance har N50m ba tare da amincewar shugaban kasa ba, da kuma zuba hannun jari da kudaden jama’a, duk da cewa cibiyar ba ta da asalin aikin samar da kudaden shiga.
“Wannan tanadi zai iya janyo matsalolin kudi da rashin da’a a gudanarwa, kuma idan aka bari, zai kafa mummunan misali ga sauran hukumomi.”
- Shugaba Bola Tinubu.
Kudurin dokar NLTF ya fuskanci matsala
Game da kudurin dokar kafa asusun dakin karatu na kasa, 2025, Shugaba Tinubu ya ce dokar na sabawa wasu dokoki da manufofin gwamnati da suka shafi yadda ake ba da tallafin kudi ga hukumomin gwamnati, tsarin haraji, da ka’idojin aiki a cikin hidimar gwamnati.
Channels TV ta rahoto Tinubu ya bayyana cewa dokar da aka tura masa “za ta haifar da tsarin da ba zai iya dorewa ba kuma zai iya zama akasin maslahar jama’a.”
“Ina fatan Majalisar Dattawa za ta gyara wadannan matsaloli domin daidaita dokokin da ka’idojin gwamnati da manufofin kudi."
- Shugaba Bola Tinubu.

Source: Twitter
Majalisa ta fara nazari kan sababbin matakai
Bayan karanta wasikun, shugaban majalisar dattawan ya yaba wa Tinubu saboda kula wajen nazarin dokoki, yana mai cewa hakan alama ce ta ingantaccen shugabanci.
“Yanzu aikinmu ne mu sake nazarin wadannan kudurorin dokoki domin tabbatar da cewa sun dace da manufofin kasa da tsarin kula da kudin gwamnati."
- Sanata Godswill Akpabio.
Ya tura dokokin biyu zuwa kwamitocin majalisa masu alaka da su don gudanar da cikakken bincike da bayar da rahoto kafin a sake duba su a zauren majalisar.
An rantsar da sababbin 'yan majalisar tarayya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya jagoranci rantsar da sababbin mambobi uku.
Sababbin mambobin sun fito ne daga zaben cike gurbi da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta gudanar ranar 16 ga Agusta, 2025.
.Yayin da aka rantsar da 'yan majalisa uku, dukkansu 'yan APC, an fadi sunayen 'yan majalisa biyu da ba su karbi rantsuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


