Sanata Nataha Ta Koma Majalisar Dattawa, Ta Zauna a Kujerar da Ta Yi Rigima da Akpabio

Sanata Nataha Ta Koma Majalisar Dattawa, Ta Zauna a Kujerar da Ta Yi Rigima da Akpabio

  • Bayan dakatarwar watanni shida, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta koma bakin aiki a zaman Majalisar Dattawa na yau Talata
  • Natasha ta isa zauren Majalisa da misalin karfe 11:52 jim kadan bayan shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karbi jagorancin zaman
  • Rahotanni sun nuna cewa Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta gaisa da wasu sanatoci kafin ta zauna a kujerarta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP), mai wakiltar Kogi Central, ta koma aiki a zauren Majalisar Dattawa a ranar Talata.

Natasha, wadda ta kammala hukuncin dakatar da ita na tsawon watanni shida, ta isa zauren majalisar da misalin ƙarfe 11:42 na safe a ranar Talata.

Sanata Natasha Akpoti.
Hoton Sanata Natasha mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa. Hoto: Natasha H. Akpoti
Source: Original

Ta shiga zauren majalisar Dattawan, sannan kuma ta nufi kujerarta, bayan ta zauna ta gaishe da wasu daga cikin sanatoci, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sunayen sababbin 'yan majalisar APC da aka rantsar yau a majalisar wakilai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aisha Yesufu ta yi wa Sanata Natasha rakiya

Ta samu rakiya daga wasu 'yan gwagwarmaya, ciki har da mai rajin Bring Back Our Girls, Aisha Yesufu, wadda aka gani a dakin masu kallo na majalisar dattawa.

Sai dai ba a bari wasu daga cikin magoya bayanta su shiga dakin masu kallo na majalisar ba.

Idan baku manta ba a ranar 23 ga Satumba, aka bufe ofishin Sanata Natasha da ke bangaren Majalisar Dattawa, wanda ya ba ta damar komawa aiki.

Bayan komawarta a watan Satumba da ya wuce, Sanata Natasha wadda aka dakatar, ta nanata cewa babu wanda za ta bai wa hakuri idan sanatoci sun dawo daga hutu.

Sanata Natasha ta gaisa da wasu sanatoci

A rahoton Premium Times, Natasha Akpoti-Uduaghan ta shiga zauren majalisar dattawa jim kaɗan bayan Sanata Godswill Akpabio, ya karɓi jagorancin zaman daga mataimakinsa, Barau Jibrin.

Sanata Natasha.
Hoton Sanata Natasha lokacin da ta isa zauren Majalisar Dattawa bayan an bude mata ofis. Hoto: Natasha H. Akpoti
Source: Facebook

Da ta iso, Sanatar ta zauna a kan kujerar da aka canza mata, wacce ta haddasa rigima tsakaninta da Shugaban Majalisar har ta kai ga daiatar da ita.

Kara karanta wannan

Akpabio ya yi maganar farko bayan bude majalisa da dawowar Sanata Natasha

Kujerar dai na ɓangaren yan adawa, gefen dama, layi na shida cikin sashe da ke da layuka bakwai a Majalisar Dattawa.

Sanye da farar riga da mayafi da kuma tabarau baki, Natasha Akpoti-Uduaghan ta gaisa daga wasu sanatoci ciki har da Seriake Dickson (PDP, Bayelsa West), Ogoshi Onawo (PDP, Nasarawa), da Gbenga Daniel (APC, Ogun ta Gabas).

Rahotanni sun nuna cewa Natasha ba ta ce komai ba ko ta gabatar da wani kudiri a rana ta farko da ta koma aiki bayan watannin da ta shafe tana karkashin hukuncin dakatarwa.

Sanata Natasha ta sake zargin Alpabio

A wani labarin, kun ji cewa bayan ta koma ofishinta, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta sake sukar shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Alpabio.

Sanata Natasha ta yi ikirarin cewa ya sha wahala matuka domin Akpabio ya mayar da ita tamkar wata 'yar aikin gidansa a Majalisar Dattawa ta 10.

'Yar majalisar dattawan, ta ce ta dauki duk abin da ya faru a matsayin kaddara, kuma hakan ya kara mata karfin gwiwar fadin gaskiya komai dacinta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262