Durkusa Matatar Dangote: An Barke da Zanga Zanga a Kaduna, an Rufe Hanyoyi
- Masu zanga-zanga sun toshe wasu manyan hanyoyi a Kaduna domin nuna goyon baya ga matatar Dangote da ke Legas
- Sun zargi masu shigo da man fetur da kuma wasu daga cikin ƙungiyoyin ƙwadago da ƙoƙarin hana ci gaban tace mai a Najeriya
- Masu zanga-zangar sun yi kira ga gwamnati ta kare masana’antun cikin gida musamman matatar Dangote daga makirci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna – A ranar Litinin, 6, Oktoba, 2025, wasu daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a Kaduna domin nuna goyon bayansu ga matatar Dangote.
Masu zanga zangar sun yi kira ga gwamnati da ta kawo ƙarshen abin da suka kira makirci na hana ci gaban tace mai a Najeriya.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa masu zanga-zangar sun fito ne karkashin ƙungiyar PANEP mai fafutukar kare tattali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote: Maganar masu zanga zanga
Jagoran ƙungiyar, Igwe Ude-Umanta, ya ce zanga-zangar na cikin jerin tarukan da aka fara a Abuja a ranar 2, Oktoba, 2025 domin ceto tattalin ƙasa daga masu son ruguza harkar tace mai.
Rahoton The Cable ya nuna cewa ya ce:
“Waɗannan ne suka lalata matatun gwamnati, suka hallaka masana’antun yadi, kuma yanzu suna ƙoƙarin hana matatar Dangote aiki. Amma ba za mu bar su ba.”
Ude-Umanta ya kwatanta halin da ake ciki da yadda aka lalata masana’antun yadi a Kaduna a da, yana mai cewa irin wannan makirci ake ƙoƙarin maimaitawa a fannin mai.
Ya zargi ƙungiyar PENGASSAN da hannu a wannan al’amari, yana kiran abin da suka yi a baya da “ta’addancin tattalin arziki.”
Kiran kungiyar ga gwamnatin Tinubu
Ƙungiyar ta bukaci gwamnatin Najeriya ta dakatar da shigo da man fetur daga ƙasashen waje ko ta sanya haraji mai tsanani don kare masana’antun cikin gida.
Ude-Umanta ya ce:
“Kasar da ke sanya haraji tana kare tattalin arzikinta. Wadanda ke shigo da mai suna tsoron gaskiya, domin tace man cikin gida zai fallasa rashin gaskiyarsu.”
Wani jagoran zanga-zangar, Dahiru Maishanu, ya ce abin da PENGASSAN ta yi ba adalci ba ne ga tattalin arzikin ƙasa.
A cewarsa:
“Ya dace gwamnati ta kama shugabannin ƙungiyar don zama darasi.”

Source: Getty Images
Kiran daukar mataki daga fadar shugaban kasa
Masu zanga-zangar sun yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar matatun cikin gida na samun danyen mai.
A cewar sanarwar:
“Dole Matatun cikin gida kamar Dangote su sami danyen mai daidai da farashin da ake ba 'yan kasashen waje domin tabbatar da dorewar kasuwanci da jawo masu zuba jari daga waje.”
ACF ta bukaci a kare matatar Dangote
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar dattawan Arewa ta ACF ta yi kira ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu kan matatar Dangote.
Kungiyar ta bukaci shugaba Tinubu ya tabbatar da ba a durkusar da matatar Dangote daga tace mai a gida Najeriya ba.
ACF ta ce wasu mutane da ke shigo da mai daga waje ne suka dauki aniyar durkusar da matatar domin cin gajiyar shigo da mai daga ketare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


