Uche Nnaji: Ministan Tinubu da Ake Zargi da Amfani da Takardun Bogi, Ya Fito Ya Yi Bayani

Uche Nnaji: Ministan Tinubu da Ake Zargi da Amfani da Takardun Bogi, Ya Fito Ya Yi Bayani

  • Ministan kimiyya da fasaha ya fito ya yi magana kan zargin da ke cewa yana amfani da takardun karatu na bogi
  • Uche Nnaji ya kare kansa inda ya nuna cewa akwai sa hannun wani gwamna don bata masa suna saboda zaben 2027
  • Ministan ya gabatar da hujjar da ke nuna cewa ya kammala karatun digiri sabanin rahotannin da ake yadawa a kansa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya yi magana kan zargin da ake yi masa na yin amfani da takardun bogi.

Uche Nnaji ya karyata zargin da aka yi masa na amfani da takardun karatu na bogi, yana mai cewa labarin da ke yawo a kafafen yada labarai an yi sa ne don bata masa suna.

Uche Nnaji ya fito ya kare kansa
Ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji. Hoto: @ChiefUcheNnaji
Source: UGC

Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin, 6 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta yi martani kan zargin Minista na amfani da takardun bogi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uche Nnaji ya yi wa duniya jawabi

Ministan ya samu wakilcin mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Dr. Robert Ngwu, a wurin taron.

Nnaji ya bayyana cewa gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ne ya kitsa wannan zargi, domin a bata masa suna kafin zaben gwamnan jihar Enugu na shekarar 2027.

Ministan ya gabatar da takarda wadda ta nuna cewa ya samu gurbi a jami’ar Nsukka (UNN) domin yin karatun Microbiology/Biochemistry a shekarar 1981, kuma ya kammala karatu a 1985 da digiri mai daraja ta uku.

Takardar da ya nuna ta saba da rahotannin kafafen yada labarai da ke cewa bai karɓi takardar kammala karatunsa ba daga jami'ar.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa jami’ar ba ta ba Ministan takardar shaidar kammala karatu ba, tana zargin cewa ya gabatar da takardu na karya lokacin tantance ministoci a shekarar 2023.

Ministan kimiyya ya gabatar da hujja

Kara karanta wannan

An bazo wa Minista wuta, Hadimin Atiku ya bukaci Shugaba Tinubu ya tsige shi nan take

Takardar da Nnaji ya gabatar a taron ta fito ne daga ofishin magatakardar Jami’ar Nsukka, Dr. (Mrs) Celine Ngozi Nnebedum, wadda IAS Onyeador ya sanya hannu a madadinta a ranar 21 ga Disamba, 2023.

An bada takardar ne bisa bukatar da Samuel Ogundipe na jaridar People’s Gazette ya turo a ranar 24 ga watan Oktoba, 2023, yana neman a tabbatar da tarihin karatun Ministan.

Ya yi nuni da cewa takardar da jaridar ta dogara da ita wajen fitar da rahoton, jami'ar ce ta bada a watan Mayun 2025 inda take ikirarin cewa babu bayanai kan kammala karatun ministan, rahoton TheCable ya tabbatar da labarin.

Uche Nnaji ya fito ya kare kansa
Ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji a ofis. Hoto: @ChiefUcheNnaji
Source: Twitter
"Daga watan Mayun 2025, wata wasika da ake zargin ta fito daga jami'ar ta bayyana, inda take ikirarin cewa babu bayanai kan kammala karatun Ministan. Tambayar da kowane dan Najeriya zai yi, ita ce mene ne ya canja daga Disamban 2023 zuwa Oktoban 2025?"

- Dr. Robert Ngwu

Nnaji ya zargi mukaddashin shugaban jami’ar na wancan lokaci kuma wanda daga baya ya zama shugaban jami’ar, da cewa ’dan jam’iyyar PDP ne da aka ba shi kwangilar aikata makirci na siyasa don bata masa suna.

Kara karanta wannan

ADC ta tanka zargin da ake yi wa ministan Tinubu na yin amfani da takardun bogi

ADC ta soki Tinubu kan ministansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu wankin babban bargo.

ADC ta caccaki shugaban kasan ne kan zargin da ake yi wa Ministan kimiyya da fasaha, na yin amfani da takardun karatu na bogi.

Jam'iyyar ta nuna cewa ba ta yi mamaki ba da Tinubu ya ci gaba da rike ministan duk kuwa da zargin da ake masa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng