ADC Ta Tanka Zargin da Ake Yi Wa Ministan Tinubu Na Yin Amfani da Takardun Bogi

ADC Ta Tanka Zargin da Ake Yi Wa Ministan Tinubu Na Yin Amfani da Takardun Bogi

  • Ana ci gaba da muhawara kan zargin da ake yi wa ministan kimiyya da fasaha na yin amfani da takardun bogi
  • Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya, ta shiga cikin sahun masu tofa albarkacin bakinsu kan zargin da ake yi wa Uche Nnaji
  • Ta yi mamakin yadda Shugaba Bola Tinubu ya ki daukar mataki duk kuwa da alamun da ke nuna cewa ya yi amfani da takardun bogi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta yi magana kan zargin da ake yi wa ministan Shugaba Bola Tinubu na yin amfani da takardun bogi.

Jam'iyyar ADC ta ce ba ta yi mamaki ba ganin cewa Tinubu ya ci gaba da rike Ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, a cikin majalisar ministocinsa.

ADC ta ragargaji Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Uche Nnaji. Hoto: @aonanuga19956, @ChiefUcheNnaji
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam'iyyar ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Litinin, 6 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ministan Tinubu zai fito bainar jama'a kan zargin amfani da digirin bogi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC ta taso Bola Tinubu a gaba

ADC ta ce rashin daukar mataki kan lamarin ya nuna cewa gwamnatin Tinubu na jurewa rashawa da rashin gaskiya.

"Ba abin mamaki ba ne cewa duk da hujjoji masu yawa da kuma fushin jama’a, Ministan kimiyya da fasaha, Mista Uche Nnaji, har yanzu yana kan mukaminsa bayan hukumomi sun nesanta kansu daga takardun da ya gabatar."

- Bolaji Abdullahi

ADC ta bayyana cewa Jami’ar Najeriya, Nsukka (UNN) da hukumar NYSC sun tabbatar da cewa ba su taba bayar da takardun da Nnaji ya gabatar ba, yayin da kotu kuma ta nuna cewa ministan ya amince da hakan a rubuce.

"Gwamnati mai da’a ba za ta yi shiru ba yayin da wani mai rike da mukamin minista ya fadi karara cewa takardunsa ba su da sahihanci. Idan ba zai yi murabus da kansa ba, me ya sa gwamnatin Tinubu ta kasa dakatar da shi?”

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ADC ta sake taso Shugaba Tinubu a gaba kan rashin tsaro

- Bolaji Abdullahi

Jam’iyyar ta kara da cewa wannan lamari yana nuna yadda APC ta saba da matsalolin takardun bogi da rashin gaskiya daga cikin manyan jami’anta, rahoton The Guardian ya tabbatar da labarin.

Ta ce hakan ya bata mutuncin gwamnatin da ke ikirarin yaki da rashawa.

"Mutunci da amincewar gwamnati suna farawa daga gaskiya da halin kirki na wadanda aka nada. Ba za a iya tsammanin ‘yan kasa su yarda da gwamnatin da ta cika da mutanen da suka yi rantsuwa bisa karya ba.”

- Bolaji Abdullahi

Jam'iyyar ADC ta ragargaji Shugaba Tinubu
Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi. Hoto: @BolajiADC
Source: Facebook

Wace shawara jam'iyyar ADC ta bada?

Jam'iyyar ADC ta bukaci a dakatar da Minista Nnaji nan take, tare da gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa.

Ta ce idan aka tabbatar da laifinsa, ya kamata a kore shi sannan a gurfanar da shi a gaban kotu saboda amfani da takardun bogi da yin rantsuwar karya.

"Yin takardun bogi ba kuskure ba ne, laifi ne. Idan an tabbatar da shi, dole ne ya fuskanci cikakken hukunci.”

Kara karanta wannan

'Ka ba mu dama': Mutanen Sokoto sun tura sako ga Tinubu kan harin ƴan bindiga

- Bolaji Abdullahi

Jam’iyyar ta yi gargadin cewa jinkirin daukar mataki daga gwamnatin Tinubu zai kara tabbatar da cewa “inganci da gaskiya ba su da matsayi a cikin tsarin shugabancinta.".

Shugaba Tinubu ya koma Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kammala ziyarar aiki da ya je yi a jihar Legas.

Shugaban kasan ya koma birnin tarayya Abuja domin ci gaba da gudanar da harkokin mulkin Najeriya.

A yayin ziyarar tasa, Shugaba Tinubu ya kaddamar da muhimman ayyuka tare da halartar tarurruka daban-daban.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng