Tinubu Ya Koma Ofis, Ya Dawo Birnin Abuja bayan Kwashe Kwanaki a Legas
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kammala ziyarar aiki da ya je gudanarwa a Mahaifarsa watau jihar Legas
- Mai girma Bola Tinubu ya kaddamar da manyan ayyuka tare da yin tarurruka da masu zuba hannun jari a yayin ziyarar tasa
- Bayan kammala ziyarar, Shugaba Tinubu ya dawo babban birnin tarayya Abuja domin ci gaba da gudanar da harkokin mulki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - A ranar Litinin, 6 ga watan Oktoban 2025, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya koma birnin Abuja bayan ziyara ta kwana 10 da ya kai jihar Legas.
Shugaba Tinubu ya gudanar da jerin manyan tarurruka tare da masu saka jari tare da kaddamar da wasu ayyuka a yayin ziyarar tasa.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin, a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubuwan da Bola Tinubu ya yi a Legas
Bayo Onanuga ya ce shugaban kasan ya isa Legas ne a ranar Juma’a, 26 ga watan Satumba, bayan halartar bikin nadin sabon Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, da aka gudanar a Ibadan.
"Yayin da yake a Legas, shugaban kasa ya gana da manyan ‘yan kasuwa, ciki har da Bayo Ogunlesi, shugaban kamfanin Global Infrastructure Partners, da kuma Keem Belo-Osagie, shugaban Metis Capital Partners kuma tsohon shugaban UBA da Etisalat."
"Har ila yau, shugaban kasa ya karɓi babban sakataren kungiyar kula da harkokin teku ta kasa da kasa (IMO), Arsenio Dominguez, tare da Ministan albarkatun teku, Adegboyega Oyetola, da shugabannin hukumomi a fannin."
"A lokacin ganawar, Tinubu ya sake tabbatar da kudirin gwamnatinsa na bunkasa fannin albarkatun teku."
- Bayo Onanuga
Shugaba Tinubu ya ziyarci jihar Imo
Sanarwar ta kara da cewa gabanin bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai, Shugaban Ƙasa ya kai ziyara zuwa jihar Imo, inda ya kaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Hope Uzodimma ya aiwatar.

Kara karanta wannan
Babu boye boye, an ji dalilin da ya sa Bola Tinubu bai jawo matarsa ta karbi musulunci ba
Ya kuma kaddamar da littafin da Gwamna Hope Uzodimma ya rubuta wanda ya bayyana tarihin shekaru 10 na jam’iyyar APC a mulki.
Tinubu ya gabatar da jawabin ranar ‘yancin kai daga Dodan Barracks, sannan ya kaddamar da sabuwar cibiyar al’adu da fasaha ta Wole Soyinka, wadda aka gyara.
A wurin taron, Shugaba Tinubu ya karfafa gwiwar ‘yan Najeriya su rika yin magana mai kyau game da kasarsu.
Tinubu ya je jana'izar mahaifiyar shugaban APC
A ranar Asabar, 4 ga Oktoba, shugaban kasa ya kai ziyara Jos, jihar Plateau domin halartar jana’izar Mama Lydia Yilwatda, mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.

Source: Twitter
A wurin jana’izar, Tinubu ya girmama marigayiyar tare da tabbatarwa kungiyoyin Kiristoci a Arewacin Najeriya, cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen adalcI da daidaito a tsakanin dukkan addinai.
ADC ta caccaki Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta ragargaji shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan rashin tsaro.
ADC ta bayyana cewa shugaban kasan bai damu da kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya ba, kamar yadda ya wajaba a kansa.
Ta nuna cewa Mai girma Tinubu ya fi maida hankali kan tarurrukan siyasa fiye da kare rayukan 'yan Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

