Kungiya Ta Jinjinawa Uba Sani kan Sabon Shirin Lafiya da Ya Kawo a Kaduna
- Kungiyar USLEPSA ta bayyana sabon tsarin agajin gaggawa na jihar Kaduna a matsayin ci gaba mai muhimmanci a fannin lafiya
- Ta ce wannan shirin ya nuna yadda Uba Sani ke kokari domin kare rayuka da tabbatar da adalci a cibiyoyin lafiya na jihar Kaduna
- Gwamna Uba Sani ya ce aikin da ya kaddamar yana cikin alkawarin sa na ganin ba a bar kowa a baya ba a fannin kula da lafiya a jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Kungiyar USLEPSA ta bayyana jin dadinta kan sabon tsarin kulawar gaggawa a fannin lafiya da Gwamna Uba Sani ya kaddamar a jihar Kaduna.
A makon da ya wuce ne gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da sabon shirin bayar da agajin gaggawa na KADSEMSAS.

Source: Facebook
Legit Hausa ta samu labari cewa a wata sanarwa da shugaban kungiyar, Kwamared Habeeb Bello Chikaji, ya sanya wa hannu, USLEPSA ta ce sabon shiri ya nuna cewa gwamnatin Uba Sani na aiki yadda ya kamata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
USLEPSA ta ce tsarin zai kawo sauyi a yadda ake bada kulawa ga marasa lafiya, musamman a lokutan da suke bukatar kulawar gaggawa da hadurra a fadin jihar.
Kungiyar USLEPSA ta yabi Uba Sani
Kungiyar ta bayyana cewa shirin KADSEMSAS ya fito da sabuwar hanyar kula da lafiya a lokacin da ake bukatar agajin gaggawa a jihar.
Ta ce ziyarar ba zata da gwamna Uba Sani ke yi a asibitoci daban-daban na nuna irin jajircewar sa wajen ganin an samar da tsarin lafiya mai inganci a jihar.
USLEPSA ta ce tsarin zai tabbatar da cewa ana kai dauki cikin lokaci, ana kare rayuka, tare da sa ido kan yadda ake gudanar da ayyukan lafiya.
Gwamna Uba Sani ya kaddamar da ofisohi
Kungiyar ta yaba da yadda gwamnatin jihar ta ofisoshin KADSEMSAS a dukkan kananan hukumomi 23, ciki har da yankunan karkara da ke fama da matsalolin lafiya.
Rahoto ya nuna cewa USLEPSA ta bayyana cewa hakan mataki ne na tarihi wanda ba a taba samun irinsa ba a jihar Kaduna.

Source: Facebook
Kira ga al’umma da karin bayanin gwamna
Kungiyar ta bukaci jama’a su taimaka wajen ganin tsarin ya yi tasiri, ta hanyar sanarwar gaggawa a kan lokaci da kuma hada kai da cibiyoyin lafiya.
A nasa jawabin yayin kaddamar da shirin, Gwamna Uba Sani ya ce:
“Wannan tsarin yana tabbatar da alkawarin mu na cewa ba za a bar kowa a baya ba — ko manomi a Ikara, ko ‘dan kasuwa a Kachia, ko dalibi a Giwa, ko kuma yaro a Kagarko.”
Gwamnan ya wallafa a Facebook cewa, bayan shekaru fiye da 10 ba tare da aiwatarwa ba, gwamnatinsa ta yi karin albashi domin karfafa ma’aikatan lafiya.

Kara karanta wannan
PENGASSAN ta jawo wa kanta, Tinubu ya dauki zafi kan rigimarta da Matatar Dangote
Legit ta tattauna da Dauda Idris
Shugaban gidauniyar GLIS ya bayyana mana cewa ya yi farin ciki da raba motocin da gwamna Uba Sani ya yi.
Kwamared Dauda Idris ya ce:
"Mu dai gaskiya mun yi murna sosai da yadda gwamna Uba Sani ya samarwa asibitoci da majinyata motocin."
"Duk wanda ya san jihar Kaduna ya san cewa gwamnan yana kokari wajen kawo cigaba."
Dauda Idris ya ce yana yi wa gwamnan fatan alheri tare da addu'ar Allah ya cika masa burinsa na siyasa da sauransu.
Za a yi bikin nadin sarauta a Kaduna
A wai rahoton, kun ji cewa masarautar Zazzau ta fitar da sanarwa kan bikin nadin sarautar Sardaunan Zazzau.
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma tsohon gwamnan Kaduna, Namadi Sambo ne aka ba sarautar.
Masarautar ta saka rana da lokacin da za a yi bikin nadin sarautar tsohon mataimakin shugaban kasar a jihar Kaduna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

