Ana Rikici kan Matatarsa a Najeriya, Dangote Ya Tafi Habasha Kafa Kamfanin Taki
- Aliko Dangote ya jagoranci kaddamar da ginin masana’antar takin zamani mai darajar dala biliyan 2.5 a garin Gode, Habasha
- Masana’antar za ta samar da ton miliyan 3 na taki a shekara tare da taimakawa bunkasa aikin gona da samar da ayyukan yi
- Firaministan kasar Habasha, Abiy Ahmed, ya ce aikin kafa masana'antar ya nuna alamar hadin kai da ci gaban nahiyar Afrika
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Habasha – Shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, ya kaddamar da ginin masana’antar takin zamani a birnin Gode da ke yankin Kudu maso Gabashin Habasha.
Masana’antar, wacce za ta kasance ta hadin gwiwa tsakanin Dangote Group da hukumar zuba jari ta Habasha, za ta rika samar da ton miliyan 3 na taki a shekara bayan kammala ta.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan kaddamar da aikin gina masana'antar ne a wani sako da kamfanin Dangote ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce aikin na da nufin amfani da albarkatu don bunkasa noma, samar da ayyukan yi, da tabbatar da wadatar abinci Afrika.
Habasha ta yaba wa Aliko Dangote
Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya bayyana masana’antar a matsayin alamar hadin kai da ci gaban kasa, yana mai cewa aikin ya yana da muhimmanci.
Punch ta rahoto ya ce:
“Wannan aikin yana nuna jajircewar mu wajen amfani da damar da muke da ita, karfafa hadin kai da tabbatar da zaman lafiya.”
Abiy ya kara da cewa manufar gwamnatin sa ita ce ta gina Habasha mai karfi da ginshikan ci gaba ta hanyar saka hannun jari cikin masana’antu da makamashi.
Dangote ya yabawa gwamnatin Habasha
Alhaji Aliko Dangote ya jinjinawa gwamnatin Abiy saboda irin sauye-sauyen tattalin arziki da ta aiwatar, wanda ya sa kasar ta zama daya daga cikin wuraren masu zuba jari a Afrika.
Ya ce:
“Hadin gwiwar mu mataki ne wajen cimma burin bunkasa masana’antu da wadatar abinci a nahiyar Afrika.”
Dangote ya kara da cewa wannan shi ne karo na biyu da kamfanin sa ke zuba jari a Habasha, bayan na masana’antar siminti da ke Mugher da ke samar da ton miliyan 2.5 a shekara.

Source: Twitter
Fa'idar kamfanin Dangote a Habasha
Dangote ya bayyana cewa bayan ginin kamfanin, za su fadada aikin zuwa samar da wasu nau’ukan taki kamar NPK da sauransu.
Ya ce cikin shekaru biyar, Habasha za ta iya zama jagorar kasashen Afrika a fannin noma da sarrafa taki.
Dangote ya kuma bayyana cewa wannan aikin zai taimaka wajen rage dogaro da shigo da kayayyaki daga kasashen waje, tare da karfafa masana’antar cikin gida.
Ya bayyana godiya ga cibiyoyin kudi kamar Afreximbank, Africa Finance Corporation, bankunan Access, First Bank da Zenith bisa tallafin su wajen aiwatar da aikin.
ACF ta nemi kare matatar Dangote
A wani rahoton, kun ji cewa dattawan Arewa sun yi zargin cewa ana shirin durkusar da matatar Dangote da ke Legas.
Rahotanni sun nuna cewa kungiyar ta yi magana ne yayin da Aliko Dangote ke bugawa da kungiyoyin mai da gas a Najeriya.
Kungiyar ACF ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da majalisar kasa su shiga lamarin wajen tabbatar da matatar ta samu kariya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


