Rashin Imami: 'Yan Yankan Kai Sun Fille Kan Tsohuwa 'Yar Shekara 69
- ’Yan sanda a jihar Anambra sun kama Obadigbo Emmanuel Anumudu da ake zargi da kisan gilla ga wata mata mai shekara 69
- An kama shi ne bayan shekara guda da ya gudu daga yankin Umueri, inda aka kashe Obianuju Akubi a watan Yulin 2024
- Rahotanni sun bayyana cewa rundunar ’yan sanda ta ce bincike yana ci gaba da gudana domin kama sauran masu hannu a laifin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Anambra - ’Yan sanda a jihar Anambra sun kama wani mutum mai shekaru 46 da haihuwa, Obadigbo Emmanuel Anumudu, bisa zargin yanke kan wata tsohuwa mai shekara 69.
Rahotanni sun bayyana cewa an yanke kan matar mai suna Obianuju Akubi ne a garin Umueri, karamar hukumar Anambra ta Gabas.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: An kama matashin da ake zargi da sace basarake a Kano, ya fara kiran sunaye

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa Anumudu ya shiga hannu ne bayan ya shafe fiye da shekara da guduwa bayan aikata laifin.
Kakakin rundunar ’yan sanda na jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da kama wanda ake zargi tare da bayyana cewa bincike yana tafiya domin cafke sauran masu hannu a kisan.
An kama wanda ya fille kan tsohuwa
Ikenga ya bayyana cewa jami’an rundunar 'yan sanda a Awkuzu ne suka kai samame a Aguleri, inda suka kama Anumudu bayan dogon bincike.
Ya ce wanda ake zargi ya dade yana buya tun bayan kisan da ya faru a ranar 22 ga watan Yuli, 2024.
“Wanda ake zargi ya amsa cewa shi ne ya kashe matar kuma ya yanke kan marigayiya Obianuju Akubi, mai shekara 69.
"Ya kuma bayyana wasu da suka taimaka masa wajen aikata wannan mummunan laifi,”
In ji Ikenga
Ina aka boye kan tsohuwar?
A yayin tambayarsa, rahoto ya nuna cewa Anumudu ya bayyana inda aka kai kan matar bayan sun kammala yanke shi.
Ikenga ya ce wannan bayanin ya taimaka wa ’yan sanda wajen gano sauran bayanai da suka shafi laifin da kuma gano sauran membobin ƙungiyar.
Ya kara da cewa rundunar tana amfani da dukkan hanyoyin bincike domin tabbatar da cewa wadanda suka tsere ba su tsira daga hukunci ba.

Source: Original
Rundunar ta ce bincike yana ci gaba
Kakakin rundunar ya tabbatar da cewa jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike don kama sauran wadanda suka tsere.
Punch ta wallafa cewa Ikenga ya kara da cewa:
“Mun kama babban wanda ake zargi, amma bincike yana ci gaba domin tabbatar da cewa duka wadanda suka aikata wannan laifi sun fuskanci hukunci.
"Za mu ci gaba da sanar da jama’a halin da ake ciki,”
Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da tsaurara matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Matsalar tsaro za ta cigaba inji gwamna
A wani rahoton, kun ji cewa wani gwamna ya yi magana kai matsalar tsaro da ta addabi Najeriya a hirar sirri.
Gwamnan ya bayyana cewa matsalar tsaro ba za ta kare yanzu-yanzu ba, duk da 'yan Najeriya ba su son jin hakan.
Ya kara da cewa akwai bukatar sauya salon yaki da 'yan ta'adda da ake a Najeriya domin kawo karshen zubar da jini a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

