'Domin Samun Sauki,' Ana Neman Tinubu Ya Saka wa Talaka Tallafi a Abubuwa 3

'Domin Samun Sauki,' Ana Neman Tinubu Ya Saka wa Talaka Tallafi a Abubuwa 3

  • Fasto Toye Ebijomore ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta tallafa wa al’umma ta hanyar rage farashin abinci da wasu abubuwa
  • Limamin cocin ya ce wannan mataki zai sa ‘yan Najeriya su daina batan sunan ƙasa su koma yin addu’a domin ci gabanta
  • Rahoto ya ce Fasto Ebijomore ya kuma bukaci a gudanar da taron addu’a na ƙasa domin neman wanzuwar albarka da zaman lafiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Fasto Toye Ebijomore ya bukaci gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta gaggauta samar da shirin tallafin abinci da abubuwa biyu.

Faston ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na Lahadi inda ya ce wannan mataki zai taimaka wajen faranta ran talakawa da kuma dawo da albarka a ƙasar.

Kara karanta wannan

'Ka ba mu dama': Mutanen Sokoto sun tura sako ga Tinubu kan harin ƴan bindiga

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu yayin wani jawabi
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu yayin wani jawabi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Leadership ta ce ya bayyana cewa idan gwamnati ta dauki wannan mataki, zai rage bakin cikin jama’a kuma ya hana su ci gaba da yin maganganu marasa kyau game da Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana son Tinubu ya sa tallafi a abubuwa 3

Ebijomore ya jaddada cewa akwai bukatar gwamnati ta taimaka wa al’umma saboda yawan kudin shiga da ake samu bai amfanar talakawa yadda ya kamata.

Ya ce:

“Najeriya ƙasa ce mai albarka, amma tana fama da laifuffuka irin su kisan kai, fasikanci da bautar gumaka, waɗanda ke hana albarkar ƙasa bayyana.”

Faston ya kara da cewa saka tallafi a harkokin abinci, kiwon lafiya da ilimi na da matuƙar muhimmanci domin inganta rayuwar ‘yan ƙasa da tabbatar da zaman lafiya.

Faston ya yi kira ga shugabanni

Ebijomore ya shawarci shugabanni su yi aiki cikin adalci da gaskiya tare da tsoron Allah domin tabbatar da cigaban ƙasa.

Ya ce:

“Shugabannin da ke kan mulki su nuna ƙauna ga Najeriya ta hanyar yin abubuwan da kasashen da suka cigaba ke yi domin walwalar jama’a.”

Kara karanta wannan

'Gadon Musulunci na yi': Tinubu ya fadi yadda yake rayuwa da matarsa Kirista

Ya kara da cewa idan shugabanni suka yi gaskiya da rikon amana, ƙasar za ta ci gaba da samun albarka daga Allah kuma mutane za su daina zagin ƙasarsu.

An nemi Tinubu ya shirya addu'o'i

Faston ya bukaci shugaba Tinubu da ya shirya taron addu’a na ƙasa domin neman gafarar Allah da dawo da ɗaukakar Najeriya.

Ya ce:

“Ya kamata mu roƙi Allah ya warkar da ƙasar nan. Ina ganin alamu na sabuwar Najeriya mai albarka da kwanciyar hankali.”
Shugaba Bola Tinubu yana yi wa jama'a bayani
Shugaba Bola Tinubu yana yi wa jama'a bayani. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ebijomore ya jaddada cewa hanya mafi dacewa don samun ci gaba ita ce tuba daga zunubai da kuma yin adalci a tsakanin shugabanni da talakawa.

Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoton, ba a samu wani martani daga fadar shugaban ƙasa ko gwamnatin tarayya ba kan wannan kira na fasto Toye Ebijomore.

Shugaba Tinubu ya ziyarci jihar Filato

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci jihar Filato domin halartar jana'iza.

Shugaban kasar ya ziyarci Filato ne domin jana'izar mahaifiyar shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda.

Kara karanta wannan

'Rashin tsaro ba zai kare yanzu ba,' Gwamna ya fadawa 'yan Najeriya gaskiya

Rahotanni sun bayyana cewa Bola Tinubu ya gana da shugabannin addinin Kirista bayan kammala jana'izar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng