Sabon Albashi: An Shiga Farin Ciki Yayin da Gwamna Ya Fara Biyan Ma'aikata N104000

Sabon Albashi: An Shiga Farin Ciki Yayin da Gwamna Ya Fara Biyan Ma'aikata N104000

  • Gwamna Hope Uzodimma ya fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na ₦104,000 ga ma’aikatan gwamnati a jihar Imo
  • Ma’aikata sun tabbatar da fara karɓar albashinsu da sabon karin, lamarin da aka ce ya sanya farin ciki a fuskokin ma'aikatan
  • Imo ta zama kan gaba a biyan albashin da ya haura ₦100,000, inda ake biyan ₦513,000 ga likitoci da ₦220,000 ga malamai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya cika alkawari, ya fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na ₦104,000 ga ma’aikatanta.

Dama can, Gwamna Hope Uzodimma ya yi alkawarin duba yiwuwar karin albashin domin tallafa wa ma’aikata a matsin tattalin da aka shiga.

Gwamna Hope Uzodimma ya fara biyan ma'aikata sabon albashi na N104,000 a Imo
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma yana jawabi a wani taro a Owerri. Hoto: @Hope_Uzodimma1
Source: Twitter

Imo: Gwamna ya kara albashin ma'aikata

Ma’aikatan gwamnati a Imo sun tabbatar da cewa sun fara karɓar saƙonnin banki da ke nuna sabon albashin, abin da ya sanya farin ciki ga ma'aikatan jihar, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindiga sun tilasta mutane barin gidajensu, garuruwa 17 sun zama kufai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wasu ma’aikata, wannan karin albashi zai taimaka musu wajen tunkarar hauhawar farashin kaya da sauran kalubalen rayuwa.

Tun da fari, Gwamna Uzodimma ya amince da biyan ₦104,000 ga sababbin ma’aikatan gwamnati, ₦513,000 ga likitoci, da kuma ₦220,000 ga malamai a makarantu na gaba da sakandare mallakar jihar.

Wannan sauyin albashi da aka samu ya sanya jihar Imo ta zamo a sahun gaba wajen kula da walwalar ma’aikata a Najeriya.

Imo ta zarce sauran jihohi a biyan albashi

Sabon tsarin albashin ya sanya jihar Imo a matakin farko a cikin jerin jihohin da ke biyan albashi mafi girma fiye da ₦70,000 da Shugaba Bola Tinubu ya amince da shi.

A cewar rahotanni, jihar Lagos ce ke biye da Imo da ₦88,000, jihar Rivers tana biyan ₦85,000, yayin da Akwa Ibom da Bayelsa ke biyan ₦80,000.

Prince Eze Ugochukwu, mai bai wa gwamna shawara kan yaɗa labarai, ya bayyana cewa sabon tsarin albashin zai ƙarfafa tattalin arzikin jihar da walwalar ma’aikata.

Kara karanta wannan

'Rashin tsaro ba zai kare yanzu ba,' Gwamna ya fadawa 'yan Najeriya gaskiya

“Manufar ƙarin albashin ita ce ƙara yawan kuɗin da ma’aikata ke samu domin su iya biyan bukatunsu da saka jari a wasu bukatun."

- Prince Eze Ugochukwu.

Ya ƙara da cewa ƙarin albashin zai haifar da ƙarin kasuwanci a cikin gida, domin karin kashe kuɗi daga ma’aikata zai motsa tattalin arziki, ya ƙara haraji, da kuma samar da ayyukan yi.

Gwamna Hope Uzodimma ya fara biyan ma'aikata sabon albashi na N104,000 a Imo
Gwamna Hope Uzodimma yana jawabi a ofishinsa da ke gidan gwamnati a Imo. Hoto: @Hope_Uzodimma1
Source: Twitter

Karin albashin zai inganta jin daɗin ma’aikata

Gwamnatin jihar Imo ta bayyana cewa wannan sabon albashin zai inganta jin daɗin ma’aikata da farfaɗo da tattalin arzikin Imo.

Ta ce wannan mataki na nuna kulawar gwamnati ne ga ma’aikata da suka kasance ginshiƙin gudanar da harkokin gwamnati da ci gaban kasa.

Sabon albashin, a cewar gwamnati, zai taimaka wajen rage hijirar ma’aikata zuwa wasu jihohi, da kuma karfafa jajircewarsu wajen gudanar da ayyukansu.

Uzodimma ya tura Musulmai 2000 Saudiyya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnatin Imo ta dauki nauyin Musulmai 200 zuwa kasar Saudiyya domin sauke farali a aikin Hajjin 2023.

Gwamna Hope Uzodimma ya jagoranci kaddamar da gidan gwamnatin jihar Imo a Owerri, inda ya karbi mutane 200 da suka amfana da shirin.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bukaci diyyar N100bn bayan tsohon kwamishina ya kira shi barawo a Facebook

An tattaro cewa wannan shine karo na farko cikin shekaru 10 da gwamnatin jihar Imo za ta dauki nauyin Musulmai zuwa aikin Hajji.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com