'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Jami'an Tsaro da Sace Mutane a Neja

'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Jami'an Tsaro da Sace Mutane a Neja

  • 'Yan bindiga sun kai wasu hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Miyagun 'yan bindigan sun yi awon gaba da mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba bayan sun farmake su da tsakar dare
  • Hakazalika, tsagerun sun hallaka wani shugaban 'yan sa-kai yayin wata arangama da suka yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - ‘Yan bindiga dauke da makamai sun kashe shugaban ‘yan sa-kai a wani harin ta'addanci da suka kai a jihar Neja.

'Yan bindigan sun kuma sace mutane bakwai a hare-hare daban-daban da suka kai a kauyukan Rijau da Magama, na jihar Nijar.

'Yan bindiga sun yi barna a Neja
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago. Hoto: @HonBago
Source: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Miyagu sun sace mutane

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Abuja, an kashe babban likita tare da sace 'ya'yansa

Majiyoyi sun tabbatar da cewa hare-haren sun faru ne a ranar Jumma'a, 3 ga watan Oktoba, 2025, a kauyukan Dukku da Shafini.

A cewar wata majiyar tsaro, da misalin karfe 9:20 na dare, ‘yan bindiga masu tarin yawa sun mamaye kauyen Dukku da ke yankin Rijau.

'Yan bindigan sun sace wani Alhaji Sodangi Mohammed da wasu mutum shida a yayin harin, sannan suka kuma tafi da su zuwa inda ba a sani ba.

Majiyoyin tsaro sun ce ana ci gaba da kokarin ceto waɗanda aka sace cikin koshin lafiya.

'Yan bindiga sun kashe shugaban 'yan sa-kai

A wani lamari daban da ya faru tun da karfe 11:00 na safiyar ranar Jumma'a, tawagar ‘yan sa-kai daga Auna da Shafini, sun yi arangama da 'yan bindiga.

Tawagar 'yan sa-kan karkashin jagorancin shugaban ‘yan sa-kai na kauyen Shafini, Yusuf Hamidu (mai shekara 40), sun gamu da ‘yan bindigan ne yayin da suke aikin sintiri.

An yi musayar wuta tsakanin bangarorin biyu, inda Yusuf Hamidu ya jikkata sakamakon harbin bindiga.

Bayan samu harbin da ya yi, an garzaya da shi zuwa asibitin gwamnati na Nasko, inda aka tabbatar da rasuwarsa bayan da aka kai shi.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindiga sun tilasta mutane barin gidajensu, garuruwa 17 sun zama kufai

'Yan bindiga sun sace mutane a Neja
Taswirar jihar Neja, tarayyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe likita

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a babban birnin tarayya Abuja.

Miyagun 'yan bindigan sun hallaka wani babban likitan dabbobi mai suna Dr. Ifeanyi Ogbu, bayan sun farmake shi a cikin gidansa da ke yankin Katampe.

Hakazalika, 'yan bindigan sun kuma yi garkuwa da 'ya'yansa guda uku wadanda har yanzu ba a san inda suka tafi da su ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng