Bayan dakatar da Sheikh Lawan Triumph, Gwamnatin Kano ta Aika Sako ga Malamai
- Majalisar Shura ta jihar Kano ta yi magana kan binciken da ake gudanarwa kan sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Lawan Shu'aibu Abubakar
- Sakataren majalisar, Shehu Wada Sagagi, ya bayyana cewa suna gudanar da bincike kan zargin yin batancin da aje yi wa malamin bisa gaskiya da adalci
- Shehu Wada Sagagi ya ja kunnen malamai kan su guji tsoma baki kan binciken da majalisar je yi don gudun jawo fitina
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Majalisar Shura ta jihar Kano ta aika da sako ga malaman addini kan binciken da ake yi dangane da Sheikh Lawan Shu'aibu Abubakar wanda aka fi sani da Sheikh Triumph.
Majalisar Shura ta gargadi malamai da sauran jama’a da su guji yin tsokaci a bainar jama’a kan binciken da ake yi wa Sheikh Lawan bisa zargin ɓatanci ga Ma'aiki.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa sakataren majalisar, Shehu Wada Sagagi, ya yi gargadin yayin wani taron manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kwanakin baya ne dai gwamnatin jihar Kano ta dakatar da Sheikh Lawan Triumph daga yin wa'azi.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta dakatar da malamin ne daga yin wa'azi domin ba shi damar zuwa gaban majalisar Shura.
Me Gwamnati ta gayawa malamai?
Shehu Wada Sagagi, ya bukaci a nuna hakuri da fahimta, yana mai jaddada cewa ana gudanar da binciken cikin gaskiya da adalci.
"Hankalin majalisar Shura ya kai kan wani sabon ci gaba da aka samu. Saboda haka muna kira ga jama’a, musamman malamai, da su daina yin magana a bainar jama’a kan wannan batu."
"Majalisar na kan lamarin, kuma duk wani mataki da za a ɗauka za a sanar da jama’a."
- Shehu Wada Sagagi
Ya kuma gargadi malamai daga wajen jihar Kano da su guji yin maganganun da ka iya tayar da hankali ko tada fitina.

Kara karanta wannan
An kwayewa minista zani a kasuwa kan gabatar da digirin bogi ga shugaba Tinubu da majalisa
"Muna kokarin ganin mun yi adalci a duk abin da muke yi. Mu ji tsoron Allah, mu kuma guji yin magana ta son rai wadda za ta iya haddasa rikici."
- Shehu Wada Sagagi
Gwamnatin Kano ta kare kanta
Shehu Wada Sagagi ya kara bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ba ta da wani son rai ko muradin siyasa a cikin lamarin, sai dai burinta shi ne a tabbatar da adalci da gaskiya.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa an kafa wani karamin kwamiti domin nazarin batutuwan da ake muhawara a kai.
"Da zarar an kammala wannan nazari, za a gayyaci Sheikh Lawan Shu’aibu Abubakar domin ya bayyana hujjojinsa da kare kansa."
- Shehu Wada Sagagi
Shugaban Malaman Kano ya yi magana kan Sheikh Triumph
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya yi magana kan tsokacin da ake yi kan maganganun Sheikh Lawan Shu'aibu Abubakar.
Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa babu tabbas kan batun cewa za a iya shawo kan lamarin ta hanyar yin baje koli tsakanin malamai.
Malamin ya bayyana cewa kowa yana ikirarin shi ne ke da gaskiya, wanda hakan ba zai sa a shawo kan rigimar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
