Abin Takaici: Rigima kan Sarautar Gargajiya Ta Lakume Rayukan Mutane a Niger

Abin Takaici: Rigima kan Sarautar Gargajiya Ta Lakume Rayukan Mutane a Niger

  • An tabbatar da mutuwar mutane biyu bayan rikici mai zafi ya barke kan sarautar gargajiya wanda ya tayar da hankulan mutane
  • An tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a kauyen Gbajibo da ke karamar hukumar Mokwa ta jihar Niger a Arewa maso Tsakiyar Najeriya
  • Iliyasu Umar Sayidi da Ahmadu Isah, dukkansu matasa daga kauyen Bukka, sun yi fada har da wukake da suka jikkata kansu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Mokwa, Niger - Hankulan al'umma sun tashi bayan rasa rayukan mutane biyu bayan barkewar rikici kan sarautar gargajiya.

Aƙalla mutane biyu ne suka mutu bayan wani rikici mai muni da ya biyo bayan takaddama kan sarautar gargajiya a jihar.

An rasa rai kan sarautar gargajiya a Niger
Taswirar jihar Niger da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton Zagazola Makama ta tabbatar da cewa lamarin ya faru a kauyen Gbajibo, cikin karamar hukumar Mokwa a jihar Niger.

Kara karanta wannan

Hare hare da kona fadarsa ya tilastawa Sarki tserewa Kamaru, mutanensa sun bi shi

Rigimar sarauta na kara yawa a Niger

Wannan ba shi ne karon farko ba da ake samun rigimar sarauta a jihar da ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

A kwanakin baya, rikicin sarauta ya barke a kauyen Muye, ta jihar Niger, bayan tsohon dagacin kauyen ya koma fada da karfi domin kwace kujerarsa da aka hana shi.

Rikicin ya kara kamari a ranar Juma'a 6 ga watan Yunin 2025 bayan magoya bayan bangarorin biyu sun yi artabu, lamarin da ya tayar da hankula.

Jami'an tsaro sun shiga tsakani da gaggawa, kuma sun tabbatar da cewa an samu daidaito, yayin da ake cigaba da sa ido a yankin don wanzar da zaman lafiya.

Yadda matasa suka rasa ransu a Niger

Wani ganau ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 3 ga Oktoba, 2025, lokacin da jayayya tsakanin wasu matasa biyu ta barke.

An bayyana sunayen matasan da Iliyasu Umar Sayidi da Ahmadu Isah dukkansu ‘yan kauyen Bukka, ta rikide zuwa fada mai tsanani.

Kara karanta wannan

An rage mugun iri: Sojojin sun sada hatsabibin dan bindiga da yaransa da mahaliccinsu

Rahotanni sun ce fadan ya rikide zuwa amfani da makami yayin da su biyun suka caka wa juna wuka, wanda hakan ya janyo mummunar rauni.

Yan sanda sun dauki mataki bayan rasa rai kan sarautar gargajiya a Niger
Sufeta-janar na yan sanda, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Matakin da yan sanda suka dauka a Niger

An garzaya da su zuwa Asibitin Gwamnati na Jebba, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu bayan isowarsu domin neman kulawar gaggawa.

‘Yan sanda sun kai ziyara wajen faruwar lamarin, inda suka ɗauki hotunan gawarwakin, sannan suka ajiye su a dakin ajiyar gawa domin yin bincike.

Hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) ya fara gudanar da cikakken bincike kan musabbabin lamarin.

Yan uwan juna suna rikici kan sarauta

A baya, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Imo ta kama wani basarake mai ikirarin gadon sarauta, Chris Obasi, a gidansa da ke Ajah a jihar Lagos.

'Yar uwarsa ta ce rikicin sarauta tsakaninsa da dan uwansa ke haddasa wannan matsala, inda ake kokarin hana gwamnatin jihar amincewa da Obasi.

Lauyansa, Farfesa Francis Dike, ya ce an zarge shi da daukar nauyin ta'addanci, amma ba za a iya ganinsa a wancan lokaci ba har sai ya dawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.