'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Abuja, an Kashe Babban Likita Tare da Sace 'Ya'yansa

'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Abuja, an Kashe Babban Likita Tare da Sace 'Ya'yansa

  • 'Yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun kai hari a babban birnin tarayya Abuja
  • Tsagerun 'yan bindigan sun farmaki gidan wani likita inda suka hallaka shi tare da yin awon gaba da 'ya'yansa
  • Kisan likitan wanda aka bayyana a matsayin jajirtacce ya sanya mutane cikin jimami da alhini

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - 'Yan bindiga sun hallaka wani likitan dabbobi da ke zaune a Abuja, Dr. Ifeanyi Ogbu, a gidansa.

'Yan bindiga sun kashe likitan ne wanda kuma shi ne tsohon shugaban kungiyar likitocin dabbobi ta Najeriya (NVMA) reshen babban birnin tarayya Abuja, a harin da suka kai.

'Yan bindiga sun kai hari a Abuja
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa ‘yan bindigan da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun kuma sace ‘ya’yansa guda uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun yi barna a Abuja

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindiga sun tilasta mutane barin gidajensu, garuruwa 17 sun zama kufai

Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa ‘yan bindigan sun kutsa cikin gidansa da ke Kubwa, a kan hanyar Kubwa–Kaduna, da daddare a ranar Jumma’a.

'Yan bindigan sun tafi da shi da kuma ‘ya’yansa uku, sannan daga baya suka jefar da gawarsa a gefen hanya.

An tabbatar da mutuwar Dr. Ogbu ne ta hannun wani abokinsa mai suna Andrew Gabriel Ikechukwu, wanda ya yi wallafa a shafinsa na Facebook.

"An samu gawar Dr. Ifeanyi Ogbu, tsohon shugaban NVMA reshen birnin tarayya Abuja, wanda aka yi garkuwa da shi tare da ‘ya’yansa uku daga gidansa a Kubwa Abuja.
"Har yanzu ba a sako ‘ya’yansa guda uku. Allah Ya shiga lamarin."

- Andrew Gabriel Ikechukwu

Marigayi Dr. Ogbu, wanda aka bayyana a matsayin kwararren likita mai jajircewa da sadaukarwa, ya rasu bar matarsa mai shayarwa da kuma ‘yan uwa cikin alhini.

Iyalan Dr. Ogbu na cikin damuwa sosai yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin gano inda ‘ya’yansa suke.

Abokai da abokan aikinsa sun bayyana mutuwarsa a matsayin rashin da ya girgiza fannin likitancin dabbobi da ma al’ummar Abuja baki ɗaya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna bayan tare matafiya a Zamfara

Har ila yau, wannan hari ya biyo bayan mutuwar wata 'yar jarida ta tashar Arise TV, Somtochukwu Maduagwu, wanda aka kashe makon da ya gabata a Katampe yayin wani hari da ake zargin masu fashi da makami suka kai.

'Yan bindiga sun kashe likita a Abuja
Dr. Ifeanyi Ogbu da 'yan bindiga suka kashe. Hoto: Andrew Gabriel Ikechukwu
Source: Facebook

Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?

Har yanzu rundunar ‘yan sanda ta babban birnin tarayya Abuja ba ta fitar da sanarwa ba, sai dai rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da gudanar da bincike.

Lokacin da aka tuntubi hukumar ‘yan sandan Abuja, ba su ɗaga kiran waya ko amsa sakon WhatsApp ba.

'Yan bindiga sun sace matafiya a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun tare matafiya a kan hanya a jihar Zamfara.

Miyagun 'yan bindigan sun yi kisa tare da tasa keyar mutane da dama wadanda ba su san hawa ba, ba su san suka ba zuwa cikin daji.

Mutanen da suka kubuta daga harin sun bayyana cewa 'yan bindigan na dauke da muggan makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng