Babu Boye Boye, An Ji Dalilin da Ya Sa Bola Tinubu Bai Jawo Matarsa Ta Karbi Musulunci ba

Babu Boye Boye, An Ji Dalilin da Ya Sa Bola Tinubu Bai Jawo Matarsa Ta Karbi Musulunci ba

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya halarci jana'izar mahaifiyar shugaban APC na kasa da aka yi yau Asabar a jihar Filato
  • A jawabinsa a cikin coci a Jos, Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa bai nemi musuluntar da matarsa, Sanata Oluremi Tinubu ba
  • Ya ce tasowa ya yi ya samu iyayensa suna bin tafarkin addinin musulunci kuma bai canza ba, amma matarsa fasto ce

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau - Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilinsa na kyale matarsa ta yi addinin kiritanci, da kuma yadda suke zaune lafiya cikin mutunta juna.

Shugaban Bola Tinubu ya ce bai taba jaraba jawo hankalin Oluremi Tinubu, uwargidan shugaban kasa, domin ta shiga addinin Musulunci ba.

Shugaba Tinubu da Oluremi Tinubu.
Hoton Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da matarsa, Sanata Oluremi. Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Tribune Nigeria ta tattaro cewa Tinubu ya ce ya yi imani da soyayya, 'yancin addini da mutunta juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Kara karanta wannan

'Gadon Musulunci na yi': Tinubu ya fadi yadda yake rayuwa da matarsa Kirista

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi wannan bayani ne a ranar Asabar a wurin jana’izar Nana Lydia Yilwatda, mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda da aka gudanar a coci a Jos, jihar Filato.

Tinubu da matarsa ba addininsu guda ba

Shugaban kasar, wanda ya isa Jos da misalin karfe 2 na rana domin halartar jana'izar, ya ce a cikin musulunci aka haife shi shiyasa ya zama musulmi.

Ya kara da cewa shi da uwargidansa suna bauta wa Allah guda daya, kuma a karshe za su amsa tambayoyi a gabanSa.

Abin da ya fi muhimmanci, a cewarsa, shi ne ayyukan mutane, halinsu da kaunar da suke nuna wa juna.

Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi hakuri da zaman lafiya a tsakaninsu, yana mai jaddada kiyayya ba ta da wani amfani.

Mai Girma Shugaban Kasa Ya kuma yi addu’a Allah ya ji kan Lydia Yilwatda tare da ba iyalinta hakuri da albarka.

Kara karanta wannan

Tazarce: An zakulo manyan abubuwa 6 da za su taimaka wa Tinubu ya ci zabe a 2027

Abin da ya hana Tinubu musuluntar da matarsa

Da yake bayanin abin da ya sa bai yi kokarin musuluntar da matarsa ba, Shugaba Tinubu ya ce.

"Duk abin da Allah ya kaddaro babu mahalukin da zai iya canza shi, ni musulmi ne, tasowa na yi naga musulunci a wurin iyaye na, kuma ban canza ba.
"Amma matata fasto ce, muna mutunta juna, tana mani addu'a, ba mu taba sabani kan addini ba. Ban taba kokarin musuluntar da ita ba saboda na yarda da 'yancin addini.
"Allah Madaukakin Sarki daya ne, duk shi muke bauta wa muna rokonsa, wata rana Shi zai mana hisabi kan ayyukan da muka aikata."
Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Hoton Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wurin taro. Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Tinubu ya yi magana kan soke faretin soji

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya ce soke faretin cikar Najeriya shekara 65 da 'yanci ya ba shi damar yin barci mai dadi a daren 1 ga Oktoba, 2025.

Tun farko, gwamnatin tarayya ta sanar da soke bikin faretin sojoji da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba domin tunawa da ranar ’yancin kai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi martani kan zargin jefa 'yan Najeriya miliyan 15 a bakin cikin talauci

Shugaba Tinubu ya ce soki faretin ya ba shi damar samun nishadi da barci mai dadi duk da dai hakan ya karya tarihin faretin ranar samun yancin kai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262