Jonathan Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Magantu kan Zargin Alakanta Buhari da Boko Haram

Jonathan Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Magantu kan Zargin Alakanta Buhari da Boko Haram

  • Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya magantu kan juya masa magana game da kungiyar Boko Haram
  • Jonathan ya musanta cewa ya taɓa danganta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ƙungiyar Boko Haram
  • Hakan ya biyo bayan yada jita-jitar cewa ya yi jawabi a taro inda ya ce Boko Haram sun zabi Buhari domin tattaunawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya yi karin haske kan rashin fahimtar maganarsa da aka yi.

Jonathan ya ce an yi masa mummunan fahimta ga kalamansa kan rawar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a rikicin Boko Haram.

Jonathan ya fayyace gaskiya kan kalamansa game da Buhari
Tsofaffin shugabannin Najeriya, Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan. Hoto: Muhammadu Buhari, Goodluck Jonathan.
Source: Twitter

Jonathan ya musanta alakanta Buhari da Boko Haram

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze ya fitar a yau Asabar 4 ga watan Oktoba, 2025, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jonathan: An fitar da dalilai kan karyata alakar Buhari da Boko Haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jonathan ya bayyana haka ne yayin da yake mayar da martani kan suka biyo bayan jawabinsa a wajen ƙaddamar da littafin tsohon CDS, Lucky Irabor.

A cikin sanarwar, Jonathan ya ce:

"Mun samu rahoton da ke yawo cewa Jonathan ya alakanta tsohon shugaban kasa, Buhari da Boko Haram a matsayin mai shiga tsakani.
"Muna son fayyace lamarin da cewa an yi wa kalaman Jonathan mummunan fahimta, babu inda ya ce Buhari yana da alaƙa da Boko Haram ko kuma goyon bayansu.
Jonathan ya wanke kansa kan alakar Boko Haram da Buhari
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Facebook

Boko Haram: Gaskiyar abin da Jonathan ke nufi

Jonathan ya bayyana cewa maganganunsa na cikin tattaunawa ne game da matsalolin tsaro a Najeriya, kuma ba wai tuhuma ba ne ga tsohon shugaban ƙasa.

Ya ce abin da ya yi nuni da shi, shi ne yadda Boko Haram ke amfani da dabarar yaudara wajen saka sunayen manyan mutane don ɓata masu suna.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

Kara karanta wannan

Bayan kalaman Jonathan, Obasanjo ya yi magana kan rikicin Boko Haram

“Abin da Jonathan ke nufi shi ne Boko Haram suna bin hanyoyin yaudara da saka sunan manya domin raba kan al'umma da kuma kashe masu ƙarfin guiwa da suke da shi kan gwamanti."

Ya bayyana cewa kalamansa misali ne na yadda kungiyar ke amfani da makirci, ba zargi ba ne ga Buhari ko wani mutum, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

"Jonathan yana nufin idan har an sanya Buhari cikin masu sasantawa to me yasa yan ta'addan ba su kawo karshen ta'addancin da suke yi ba lokacin da ya zama shugaban ƙasa?.
"Domin cire shakku a zukata, Jonathan ya yabawa Buhari kan kokarin da ya yi wurin yaki da ta'addanci inda ya ce har shi kansa marigayin bai tsira daga hare-harensu ba."

- Cewar sanarwar

A ƙarshe, ofishinsa ya roƙi jama’a da su yi watsi da duk wani labari da ke karkatar da gaskiya, yana mai cewa Jonathan na kishin zaman lafiya da haɗin kai.

Buhari: An soki kalaman Jonathan kan Boko Haram

Mun ba ku labarin cewa kalaman tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan kan marigayi Muhammadu Buhari sun fara tauyar da kura.

Kara karanta wannan

Jonathan ya debo ruwan dafa kansa da ya jingina Marigayi Buhari da Boko Haram

Jonathan ya ce akwai lokacin da Boko Haram ta gabatar da Buhari a matsayin wakilinta a tattaunawar sulhu da gwamnatin tarayya.

Tsohon kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya ce ikirarin Jonathan ba gaskiya ba ne, wani salo ne na neman kuri'u a 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.