‘Gadon Musulunci Na Yi’: Tinubu Ya Fadi Yadda Yake Rayuwa da Matarsa Kirista

‘Gadon Musulunci Na Yi’: Tinubu Ya Fadi Yadda Yake Rayuwa da Matarsa Kirista

  • Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ja hankalin yan Najeriya game da zaman lafiya musamman a tsakanin mabambantan addinai
  • Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su guji bambancin addini da kabilanci, yana mai cewa ƙauna da zaman tare su ne ginshiƙan ci gaba
  • Gwamna Caleb Mutfwang ya gode wa Tinubu bisa halartar jana’izar mahaifiyar shugaban APC, yana mai jaddada kudurin gwamnati domin zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga al’ummar Jihar Plateau da ma ‘yan Najeriya baki ɗaya su zauna lafiya.

Shugaban kasar ya bukaci hakan domin dorewar zaman lafiya tare da yin aiki don ci gaban ƙasa baki daya.

Tinubu ya fadi yadda yake raywua da matarsa Kirista
Shugaban kasa, Bola Tinubu da mai dakinsa, Sanata Oluremi Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Tinubu ya ja hankalin Musulmi da Kirista

Tinubu ya yi wannan jawabi ne a lokacin jana’izar Nana Lydia Yilwatda, mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda, a garin Jos, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Rashin tsaro ba zai kare yanzu ba,' Gwamna ya fadawa 'yan Najeriya gaskiya

Shugaban ya ce shi Musulmi ne kuma gado ya yi amma bai sauya addininsa ba yayin da matarsa ke yi addininta daban.

Ya ce:

“Na gaji addinin Musulunci daga iyayena, amma matata fasto ce, kuma tana yi min addu’a a kowane lokaci.
"Ban taɓa tilasta mata ta canza addini ba saboda na yarda da ‘yancin addini kowa zai yi wanda yake so."
“Muna yin addua'a bauta ga Ubangiji guda ɗaya, mai iko, zamu amsa abin da muka yi gare shi bisa ayyukanmu da halayenmu.”

Shugaban ƙasar ya jaddada cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne ƙaunar juna da zaman lafiya, domin kowa zai amsa tambayoyin Allah bisa ayyukansa da halayensa.

Mutfwang ya karbi bakuncin Tinubu a Plateau
Gwamna Caleb Mutfwang jihar Plateau yayin taro a gidan gwamnati. Hoto: Caleb Mutfwang.
Source: Facebook

Jawabin Gwamna Mutfwang bayan ziyarar Tinubu

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya gode wa shugaban ƙasa bisa halartar jana’izar dattijuwar wacce ta rasu a kwanakin baya.

Mutfwang ya jaddada cewa gwamnatinsa ta ɗauki matakan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Kara karanta wannan

Matasa sun yi zanga zangar tir da kalaman Gwamnan Kano na a cire kwamishinan 'yan sanda

Haka kuma, ya gode wa uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, bisa taimakon da take baiwa mata da yara da ke gudun hijira a jihar.

Shugaban APC ya fadi halayen mahaifiyarsa

A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana mahaifiyarsa a matsayin mace mai jajircewa.

Har ila yau, ya ce dattijuwar ta kasance mai sadaukarwa da ƙaunar al’umma, wacce ta rayu tana taimakon maƙwabta da marasa ƙarfi, cewar rahoton Punch.

Ya gode wa shugaban ƙasa, gwamnoni, ‘yan majalisa, da al’ummar Najeriya baki ɗaya bisa tausayawa da goyon baya a lokacin da iyalinsa ke cikin jimami.

An birne marigayiyar, wacce ta rasu tana da shekaru 83 a duniya, a Dungung, ƙaramar hukumar Kanke da ke jihar Plateau.

'Na fuskanci kalubale': Matar Tinubu kan zaben 2023

Kun ji cewa mai dakin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ta bayyana halin da ta tsinci kanta a ciki game da zaben shekarar 2023.

Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana cewa ta fuskanci kalubale daban-daban lokacin zaben da kuma kafin a rantsar da shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya cire kunya ya fadi abin da ya gaza yi a rayuwarsa a gaban 'yan APC

Ta nuna cewa ta sha yin tunani kan cewa ko za ta iya sauke nauyin da zai hau kanta na zama uwargidan shugaban kasa a irin wannan kasa ta Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.