Kotu Ta Yi Hukunci kan Dakatarwar da Majalisa Ta Yi Wa Sanata Natasha
- Babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja, ta yanke hukunci kan karar da ke kalubalantar dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
- An shigar da karar ne don nuna rashin yadda da matakin da Majalisar Dattawa da dauka na dakatar da Sanata Natasha
- Alkalin kotun, mai shari'a James Omotosho, ya yanke hukunci kan karar a ranar Jumma'a 3 ga watan Oktoban 2025
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar kan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Karar ta kalubalanci halaccin dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida saboda zargin rashin da’a.

Source: Facebook
Jaridar Tribune ta rahoto cewa alkalin kotun, mai shari'a James Omotosho ne ya yanke hukuncin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta yi watsi da karar Natasha
An shigar da karar ne da ke kalubalantar dakatar da Sanata Natasha ta hannun Ovavu Illiyasu da wasu mutane tara.
Sai dai, alkalin kotun ya yi watsinda karar, yana cewa masu shigar da ita, ba su da hurumin doka don kawo irin wannan lamari gaban kotu.
An kalubalanci dakatar da Natasha
A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/654/2025, masu shigar da ita sun kalubalanci sahihancin dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bisa dalilai daban-daban, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da labarin.
A cikin bukatunsu, masu karar sun roki kotu ta soke dakatarwar, suna mai cewa yankinsu na Kogi ta Tsakiya zai rasa wakilci a Majalisar Dattawa, kuma suka nemi a dawo da ita nan take.
Sun gabatar da hujjoji masu yawa don goyon bayan karar, ciki har da cewa dakatarwar ta tauye wa jama’ar yankin damar samun wakilci yadda ya kamata a majalisa.
Amma yayin da yake yanke hukunci a ranar Jumma’a, Mai shari’a James Omotosho ya ce babu hurumin doka ga masu karar don su shigar da ita, don haka ya yi watsi da shari’ar saboda rashin inganci.

Kara karanta wannan
Kurunkus: Kotu ta yanke hukunci kan ingancin dokar ta bacin da Tinubu ya sa a Ribas
Sanata Natasha ta koma majalisa
A halin yanzu, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta koma ofishinta a Majalisar Dattawa a ranar 23 ga Satumba 2025, bayan kammala dakatarwarta ta watanni shida.
An dakatar da ita ne tun ranar 6 ga watan Maris 2025, bisa zargin ta karya dokokin cikin gida na majalisa.

Source: Twitter
Duk da haka, ta ci gaba da bayyana cewa ba ta taɓa sakaci da ayyukanta a matsayin Sanata ba.
Majalisar Dattawa ta buɗe ofishinta da aka rufe tsawon watanni shida yayin dakatarwar.
Dawowarta ta jawo farin ciki da goyon baya daga magoya bayanta, waɗanda suka raka ta daga babbar kotun tarayya Abuja.
Sanata Natasha ta zargi Akpabio
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi zarge-zarge kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Sanata Natasha ta yi zargin cewa shugaban Majalisar Dattawan ya mayar da ita kamar 'yar aikin gidansa.
Ta kara da cewa ta dauki dakatarwar da aka yi mata a matsayin kaddara, kuma hakan ya kara mata karfin gwiwar ci gaba da fadin gaskiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

