'Yan Bindiga Sun Tafka Barna bayan Tare Matafiya a Zamfara
- 'Yan bindiga sun yi ta'asa a wani harin da suka kai a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
- Miyagun 'yan bindigan sun tare wasu matafiya ne a hanyar Mayanchi-Anka inda suka yi kisa tare da sace mutane masu yawa
- Mutanen da suka samu tsira daga harin sun yi bayanin cewa 'yan bindigan sun tare hanyar ne dauke da muggan makamai
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun kai wani mummunan hari da Yammacin ranar Juma’a, 3 ga watan Oktoban 2025 a jihar Zamfara.
‘Yan bindigan sun kai mummunan harin ne inda suka kashe tare da sace mutane da dama a jihar Zamfara.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Mayanchi–Anka, da ke jihar Zamfara.
'Yan bindiga sun tare matafiya a Zamfara
‘Yan bindigan sun tare hanyar sannan kuma suka gudanar da ta’addancinsu na kashe mutane da yin awon gaba da wasu zuwa cikin daji.
Wani direba da ya tsira daga harin, Malam Muhammad Ahmad, ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun kasance suna dauke da muggan makamai.
"Yan bindigan sun tare mu a hanya sannan suka sace mutane da yawa. Wasu daga cikinmu sun watse inda muka tsere cikin daji."
"Mutanen da suka tsira su ne waɗanda suka ɓuya a cikin dajin inda aka shuka amfanin gona masu tsawo."
"An kashe abokina Abubakar Lawali Sardauna saboda ya ƙi yarda a yi garkuwa da shi, yana cewa ba zai bi ‘yan bindigan zuwa cikin daji ba."
- Malam Muhammad Ahmad
Ba a samu jin ta bakin 'yan sanda ba
Legit Hausa ta yi kokarin tuntuɓar mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar.
Sai dai, kakakin 'yan sandan bai dauki kiran da aka yi masa a waya ba, sannan kuma bai kira ba har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoton.
Hare-haren 'yan bindiga sun zama ruwan dare a jihar Zamfara, inda ake kashe mutane tare da yin garkuwa da wasu zuwa cikin daji.

Source: Original
Lamarin ya jawo rasa rayukan dubunnan mutane da suka hada da mata, maza da kananan yara, yayin da aka raba mutane da dama da muhallansu.
Hare-haren na 'yan bindiga sun sanya mutane da dama yin gudun hijira daga wuraren da suka saba gudanar da rayuwarsu.
Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga
- DSS sun kwace makaman yan sa kai kafin harin yan bindiga? Gwamnati ta magantu
- 'Yan bindiga sun kai kazamin hari, an rasa rayukan jami'an tsaro a Kwara
- 'Yan bindiga sun hallaka dan sanda, an yi awon gaba da jami'an tsaro
'Yan bindiga sun yi aika-aika a Kwara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.
'Yan bindigan sun hallaka mutane fiye da 10 da suka hada har da basarake da jami'an tsaro na 'yan sa-kai.
Hakazalika, miyagun sun kona gidaje da shaguna tare da yin awon gaba da mutane masu yawa a yayin harin da suka kai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

