"An Ci Amanata": Remi Tinubu Ta Fadi Halin da Ta Shiga kan Zaben 2023
- Uwargidan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ta bayyana halin da ta tsinci kanta a ciki game da zaben shekarar 2023
- Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana cewa ta fuskanci kalubale daban-daban lokacin zaben da kuma kafin a rantsar da shugaban kasa
- Ta nuna cewa ta sha yin tunani kan cewa ko za ta iya sauke nauyin da zai hau kanta na zama uwargidan shugaban kasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi magana kan kalubalen da ta fuskanta kafin hawa kan kujerar da ta kai a yanzu.
Oluremi Tinubu ta bayyana cewa ta kasance cike da tsoro, shakku da kadaici, waɗanda suka sa ta fara tambayar kanta ko tana da shirin da ya dace domin ɗaukar nauyin zama uwargidan shugaba kasa a kasa mafi yawan jama’a a Afrika.

Source: Twitter
An kaddamar da littafin Remi Tinubu
Jaridar The Punch ta ce Remi Tinubu ta bayyana hakanne a cikin littafinta mai shafi 52 mai suna 'The Journey of Grace: Giving Thanks in All Things'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fitar da littafin ne domin bikin cikar shekaru 65 da haihuwar uwargidan shugaban kasan a duniya, rahoton TheCable ya tabbatar da hakan.
Uwargidan shugaban kasan ta bayyana cewa matsin lamban da ta fuskanta, ya karu ne bayan zaɓen 2023.
Sanata Remi Tinubu ta shiga shakku
Remi Tinubu ta bayyana cewa sau da yawa tana jin ba ta shirya ba sosai don yin aikin uwargidan shugaban kasa a kasar da ke da mutane sama da miliyan 240.
"Ni kaina, na kasance ina cike da ruɗani, ina tambayar kaina ko ina da shiri da kwarewar da za su sa na iya yin aikin uwargidan shugaban kasa a kasa mai girma kamar tamu yadda ya kamata."
"Kasar da ke da mutane fiye da miliyan 240 daga al’adu, kabilu, harsuna da addinai daban-daban."
"Na shafe kwanaki ina kebewa, ina tunanin ko zan iya taka rawar bada goyon baya da haɗin kai ba tare da yin kuskure ba."
- Remi Tinubu
Wane hali Remi Tinubu ta shiga a 2023?
Remi Tinubu ta kuma bayyana cewa a ranakun bayan zaɓen shugaban kasa da kafin rantsar da mijinta a ranar 29 ga Mayu, 2023, ta kan kasance tana kuka a ɓoye saboda jin wasu aminanta da ta taɓa amincewa da su a siyasa sun yaudare ta.

Source: Twitter
“Bayan zaɓukan 2023, kafin ranar rantsuwa a ranar 29 ga Mayu, 2023, lokacin ne zuciyata ta fara tunani."
"Wasu ‘yan Najeriya daga fannoni daban-daban, musamman Kiristoci, sun ki amincewa da sakamakon zaɓen shugaban kasa."
"Duk da nasarar da muka samu, na ji kamar ni kaɗai ce, ina kuka a boye, ina tambayar kaina dalilin da ya sa wasu daga cikin waɗanda na ɗauka a matsayin aminai da ‘yan uwa suka yaudare ni, waɗanda na taɓa bari suka san gidana da iyalina."
- Remi Tinubu
Remi Tinubu ta samu sarauta
A wani labarin kuma, kun ji cewa uwargidan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta samu sarauta a jihar Gombe.
Oluremi Tinubu ya samu sarautar Sarauniyar Yakin Akko a masarautar Akko daga jihar Gombe.
Masarautar ta jinjinawa uwargidan shugaban kasan bisa irin ayyyukan da take gudanarwa kan talakawan Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


