Gwamnan Bauchi Zai Kirkiro Masarautu, Mutane 13 Za Su Dawo Sarakuna
- Kwamitin gwamnati a Bauchi ya ba da shawarar ƙirƙirar sababbin masarautu 13 da wasu gundumomi a fadin jihar
- Shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya mika rahoton ga gwamna Bala Mohammed a ranar 4, Oktoba, 2025
- Gwamnan ya yaba da aikin kwamitin, yana mai cewa tsarin zai inganta shugabanci da zaman lafiya a Bauchi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi – Gwamnatin jihar Bauchi na shirin aiwatar da gyara a tsarin gargajiya bayan kwamitinta ya gabatar da rahoto kan ƙirƙirar sababbin masarautu.
Kwamitin, wanda aka kafa don nazarin buƙatun al’ummomi, ya bada shawarar ƙirƙirar sababbin masarautu 13.

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayanai kan rahoton ne a wani sako da hadimin gwamnan, Lawal Muazu Bauchi ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya samu amincewar Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed wanda ya bayyana godiya ga yadda aka gudanar da aikin cikin gaskiya da cikakken bincike.
Masarautun da za a kirkira a Bauchi
Shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya bayyana cewa sun karɓi takardu 196 daga al’ummomi daban-daban, ciki har da buƙatun ƙirƙirar masarautu 17 da hakimai 166.
Ya ce bayan nazari da tantancewa, kwamitin ya ba da shawarar ƙirƙirar sababbin masarautu 13, yankuna biyu da hakimai 113 waɗanda suka fi cancanta.
A cewarsa, an gudanar da aikin bisa adalci da hangen nesa na tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai, da wakilcin kowa.
Martanin Gwamna Bala Mohammed
Da yake karɓar rahoton, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya jinjinawa kwamitin bisa aikin da ya kira mai gaskiya da cikakken tsari.
Ya ce tsarin ya dace da manufar gwamnatinsa ta “bunƙasa Bauchi” domin sauƙaƙa shugabanci da kawo karshen yankunan da ba a kula da su.
Gwamnan ya ce:
“Kodayake wannan gyara na iya zama maras dadi ga wasu sarakuna, amma an yi irin haka a wasu jihohi da ƙasashe domin bunƙasa al’umma.”

Source: Twitter
Manufar kirkirar masarautun a Bauchi
Gwamnan Bauchi ya ce gwamnati za ta aiwatar da shawarwarin kwamitin cikin adalci, ta yadda sabbin al’ummomi za su samu wakilci ba tare da tauye mutuncin tsofaffin masarautu ba.
Tribune ta wallafa cewa ya bayyana cewa manufar gyaran ita ce samar da ƙarin dama ga shugabannin gargajiya da kuma haɓaka ci gaban yankuna.
Haka kuma ya yi alkawarin mika rahoton kai tsaye ga majalisar dokokin jihar domin duba shi da gaggawa ba tare da son rai ba.
Gwamnan ya roƙi majalisar dokoki da ta hanzarta aikin duba rahoton ba tare da nuna bambancin addini ko siyasa ba.
Makiyaya sun hana noma a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa ana cigaba da samun sabani tsakanin manoma da makiyaya a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan
Matasa sun yi zanga zangar tir da kalaman Gwamnan Kano na a cire kwamishinan 'yan sanda
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin na faruwa ne a karamar hukumar Darazo, inda mutane suka gaza zuwa gona.
Legit Hausa ta tattauna da mutane da dama a yankin kuma sun bayyana cewa suna bukatar gwamnati ta magance matsalar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

