Mai Mala Buni Ya Gwangwaje Dan Tsohon Gwamna da Mukami a Gwamnatinsa
- Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya bada mukami ga dan marigayi Bukar Abba Ibrahim wanda ya taba rike madafun ikon jihar
- Mai Mala Buni ya amince da nadin babban dan marigayin a matsayin daya daga cikin masu ba shi shawara na musamman, domin gudanar da mulkin jihar
- A cikin sanarwar da aka fitar kan nadin, an bayyana cewa zai fara aiki ne nan take ba tare da bata wani lokaci ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya naɗa ɗan marigayi tsohon Gwamna Bukar Abba Ibrahim, mukami a gwamnatinsa.
Gwamna Mai Mala Buni ya amince da nadin Mohammed Bukar Abba Ibrahim, a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kananan hukumomi.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ce sanarwar nadin ta fito ne daga bakin sakataren gwamnatin Yobe, Baba Mallam Wali, wacce aka rabawa manema labarai a Damaturu, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan
Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bukar Abba Ibrahim ya yi gwamna a Yobe
Mohammed Bukar Abba Ibrahim wanda aka fi sani da Abbati, shi ne babban ɗan tsohon gwamnan.
Marigayi Bukar Abba Ibrahim ya taba mulkar jihar Yobe daga watan Janairun 1992 zuwa Nuwamban 1993 a Jamhuriya ta uku.
A shekarar 1999 ya zama zababben gwamnan jihar Yobe karkashin jam'iyyar ANPP, inda ya yi wa'adi biyu kan mulki.
Hakazalika, ya yi sanatan Yobe ta Gabas tun daga 2007 har zuwa shekarar 2019.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairun 2024 a wani asibiti da ke kasar Saudiyya, bayan ya sha fama da jinyar rashin lafiya.
Gwamna Buni ya ba dan Bukar mukami
A cewar sanarwar, Mohammed Bukar Abba Ibrahim ya taɓa rike mukamin mai ba Gwamna Buni shawara na musamman kan zuba jari.
A yayin da yake kan wannan mukamin, ya taka muhimmiyar rawa wajen kirkiro da shirye-shiryen da suka bunkasa samun damarmaki a bangaren tattalin arzikin jihar Yobe da kuma jawo hankalin masu zuba jari daga ɓangaren 'yan kasuwa masu zaman kansu.

Kara karanta wannan
Gwamna ya bukaci diyyar N100bn bayan tsohon kwamishina ya kira shi barawo a Facebook
Gwamna Buni ya bayyana cewa wannan naɗin yana cikin manufar gwamnatinsa ta sanya matasa cikin harkokin mulki, domin ba su dama su taka rawa wajen kawo ci gaba a jihar.

Source: Facebook
Hakazalika, Gwamna Buni ya sha jaddada muhimmancin matasa a cikin muhimman matakan yanke shawara, yana mai cewa makomar jihar Yobe tana cikin kirkira, fasaha da jajircewar matasanta.
Sanarwar ta kara da cewa nadin ya fara aiki nan take.
Jigon APC ya fice daga jam'iyyar a Yobe
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani sanannen dan siyasa kuma babban jigo a APC a jihar Yobe, Hon. Mohammed Bello, ya fice daga jam'iyyar mai mulki.
Sanannen dan siyasan ya bayyana matakin da ya dauka na ficewa daga jam'iyyar APC a matsayin raba kansa daga cikin kangin da yake ciki.
Hon. Bello Mohammed wanda ya taba yin takarar Sanatan Yobe ta Arewa karkashin APC, ya bayyana cewa ficewarsa daga jam'iyyar ta fara aiki ne nan take.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng