Tayin da Matatar Dangote Ta Yi Wa PENGASSAN kan Ma'aikatan da Ta Kora

Tayin da Matatar Dangote Ta Yi Wa PENGASSAN kan Ma'aikatan da Ta Kora

  • Korar ma'aikatan da matatar Dangote ta yi ya jawo rikici tsakaninta da kungiyar manyan ma'aikatan man fetur ta kasa (PENGASSAN)
  • Rikicin ya jawo kungiyar tsunduma cikin yajin aiki tare da bada umarnin daina kai iskar gas da danyen fetur ga matatar Dangote
  • Sai dai, a yayin tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, matatar Dangote ta yi wa PENGASSAN wani tayi kan ma'aikatan da ta kora

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sababbin bayanai sun fito kan tattaunawar da aka yi tsakanin matatar Dangote da kungiyar PENGASSAN.

Tattaunawar dai ta gudana ne bayan rikicin da ya biyo bayan korar wasu ma’aikata da matatar Dangote ta yi.

PENGASSAN ta ki amincewa da bukatar Dangote
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar Premium Times ta bayyana cewa wasu majiyoyi sun yi mata bayana kan wasu abubuwan da suka faru yayin tattaunawar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani tayi Dangote ya yi wa PENGASSAN?

Kara karanta wannan

Yadda sakon WhatsApp ya jawo matatar Dangote ta kori ma'aikata 800

Sababbin bayanai daga cikin tattaunawar sun bayyana cewa matatar Dangote ta amince da biyan ma’aikatan da aka kora albashin shekara biyar ba tare da yin aikin komai ba.

An yi wannan tayin ne saboda damuwar da matatar ke da ita game da yiwuwar samun zagon kasa daga wasu daga cikin ma’aikatan da aka sallama.

Wadanda suka san yadda zaman ya gudana sun bayyyana cewa matatar ta yi wannan tayin ne yayin tattaunawar.

"Za a bar ma’aikatan su zauna a gidajensu ko su ci gaba da neman wasu ayyuka, amma za su rika karɓar albashinsu kowane wata na tsawon shekaru biyar."

- Wata majiya

Majiyoyin sun kara da cewa duk da cewa wakilan gwamnati sun nuna damuwa kan nauyin kuɗi da irin wannan tsarin zai jawo, matatar Dangote ta dage cewa hakan ya fi sauki gare ta fiye da barin mutanen da ba ta yarda da su ba su shiga wurin aiki.

PENGASSAN ta ki amincewa da tayin

Sai dai majiyoyin sun bayyana cewa ƙungiyar PENGASSAN ta ki yarda da wannan tayin, inda ta fi son ma’aikatan da aka kora su koma aiki a wasu rassan Dangote maimakon zama a gida.

Kara karanta wannan

Rikici ya kare: Gwamnati ta shawo kan sabanin Dangote da PENGASSAN

"Dangote ya bayar da tayin biyan waɗanda aka kora albashi na shekara biyar suna zaune a gida, ko kuma suna yin wasu abubuwa daban, amma ba za su kusanci matatar ba saboda tsoron zagon kasa."
"Duk da cewa wakilan gwamnati sun ce hakan na iya zama nauyi ga Dangote, kamfanin ya ce hakan ya fi masa sauƙi fiye da barin mutanen da bai yarda da su ba, su shiga wurin aiki, saboda ba ya son zagon kasa. Amma PENGASSAN ta ki amincewa."

- Wata majiya

Matatar Dangote ta so biyan ma'aikatan da ta kora albashin shekara 5
Hoton wani bangare na matatar Dangote. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Me kungiyar PENGASSAN ta ce kan lamarin?

Lokacin da aka tuntubi babban sakataren PENGASSAN, Lumumba Okugbawa, domin sanin dalilin kin amincewa da tsarin biyan albashi ba tare da aiki ba, ya bayyana cewa sun cimma matsaya wacce ta fi bai wa jin dadin ma’aikata muhimmanci.

Okugbawa ya ce tattaunawar ta kasance tsarin bayarwa da karɓa, inda aka tattauna zaɓuɓɓuka daban-daban kafin a cimma yarjejeniyar da duka ɓangarorin suka gamsu da ita.

Ya jaddada cewa matsayar karshe ce ta fi muhimmanci, ba zaɓuɓɓukan da aka tattauna a baya ba.

"Don haka, batun da yake cewa zai biya albashi na shekara biyar ba tare da aiki ba, ban ga muhimmancin wannan zaɓi ba a matakin karshe."

Kara karanta wannan

Dangote: 'Yan kwadago sun hade kai, NLC na shirin taya PENGASSAN a rufe Najeriya

"Abu mafi muhimmanci shi ne, me ku ka amince da shi a karshe? Shi ne za a aiwatar, ba abin da aka ki amincewa da shi ba."

- Lumumba Okugbawa

Yajin aikin PENGASSAN ya jawo asara

A wani labarin kuma, kuma kun ji cewa kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), ya bayyana asarar da yajin aikin kungiyar PENGASSAN ya jawo.

Shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari, ya bayyana cewa yajin aikin ya kawo tsaiko wajen hakar danyen mai, iskar gas da samar da wutar lantarki.

Ojulari ya bayyana cewa sama gangar danyen mai 283,000 aka kasa hakowa a ranar farko da aka fara yajin aikin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng