Bayan Soke Fareti, Tinubu Ya Fadi abin da Ya Faru da Shi a Daren 1 ga Oktoba 2025
- Shugaba Bola Tinubu ya ce soke faretin cikar Najeriya shekara 65 da 'yanci ya ba shi damar yin barci mai dadi a daren 1 ga Oktoba, 2025
- Shugaban kasar, ya kuma ce ya samu damar jin daɗin karin kumallo a ranar Laraba, har ya shirya zuwa kaddamar da cibiyar Wole Soyinka
- Tinubu ya bayyana Wole Soyinka a matsayin babbar kadara ga Najeriya, yana mai cewa ya ba da gudummawa wajen kwato 'yancin kasa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi bayani game da soke faretin da aka saba yi na bikin murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yancin kai.
A cewar shugaban kasar, soke faretin ranar 1 ga Oktoba ya ba shi damar yin barci mai dadi tare da jin daɗin karin kumallo a safiyar Laraba.

Source: Twitter
Gwamnati ta soke faretin ranar 'yanci
A cewar jaridar Daily Trust, gwamnatin tarayya ta sanar da soke bikin faretin sojoji da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025 domin tunawa da ranar ’yancin kai.
Sanarwar sokewar bikin ta fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF) a ranar Litinin, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.
Sakataren gwamnatin ya jaddada cewa ba a soke faretin da nufin rage muhimmancin bikin shekara 65 da samun ’yancin kan Najeriya ba.
Sanarwar ta ce:
"Gwamnatin Tarayya na sanar da soke bikin tunawa da ranar ’yancin kai ta bana da aka tsara gudanarwa ranar Laraba, 1 ga Oktoba. Wannan mataki ba ya nufin rage darajar wannan muhimmiyar rana a tarihin kasa."
Tinubu ya gode wa CBN da kwamitin BC
Tinubu ya yi jawabi game da soke fareti ne yayin da yake jawabi a wurin taron kaddamar da sabuwar cibiyar al'adu da kere-kere ta Wole Soyinka a Legas.
A wajen kaddamar da cibiyar, wacce aka fi sani a baya da cibiyar NAT, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya samu hutu sosai bayan soke bikin faretin.
Ya kuma bayyana cewa an samu karin nishaɗi a bikin kaddamar da cibiyar, wacce CBN tare da kwamitin ma'aikatan bankuna suka dauki nauyin gyara da sabuntawa.
“Na samu barci mai dadi” – Tinubu
Tinubu ya bayyana farin cikinsa kan yadda aka sake bude ginin, wanda ya ce ya cancaci sunan Wole Soyinka, gwarzon marubuci kuma mai lambar yabo ta duniya.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce:
"Na gode kwarai da wannan daren. Na yi barci cikin salama, na yi karin kumallo mai dadi sannan na jira lokacin wannan bikin. Na aiwatar da abubuwa masu muhimmanci a daren nan."
Ya kara da cewa wannan ya karya tarihin jerin gwanon shagulgulan faretin sojoji da aka saba yi a duk ranar zagayowar ’yancin kai.

Source: Twitter
Wole Soyinka a matsayin gwarzon kasa
Da yake yabon marubucin, Tinubu ya ce Wale Soyinka babbar kadara ce ga duniya, musamman Najeriya, wanda ya bayar da gudummawa wajen gina kasa da kuma fafutukar ’yanci.

Kara karanta wannan
Gwamna Fintiri ya yi afuwa ga masu laifi don murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun 'yanci
A sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, Tinubu ya ce:
"Na tabbatar babu wani suna da ya dace da wannan gini face 'Cibiyar Wole Soyinka,' kuma ya zama dole a yi hakan."
Manyan bakin da suka halarci bikin sun hada da uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, Gwamna Babajide Sanwo-Olu, Godswill Akpabio, da kuma sarkin Kano Muhammadu Sanusi II tare da Farfesa Wole Soyinka wanda aka karrama.
'An fara samun sauki a Najeriya' - Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya ce lokacin matsananciyar wahala ta kau a Najeriya, za a fara ganin ribar manufofinsa.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi ga 'yan kasa kan cikar kasar nan shekaru 65 da samun 'yancin kai daga Turawa.
A cewarsa, Najeriya ta fara fitowa daga cikin mawuyacin halin tattalin arziki da ta tsinci kanta ciki a baya, tare da yi wa jama'a albishir.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

