Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu Ta Samu Sarauta a Gombe
- Masarautar Akko da ke jihar Gombe ta saka wa Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu saboda ayyukan ci gaban talaka da ta ke yi
- Mai Martaba, Lamidon Akko, Alhaji Umar Muhammad Atiku ya nada Sanata Remi a matsayin Sarauniyar Yakin Akko saboda wadannan ayyukan
- A jawabinta na godiya, Uwargidan Shugaban Kasan ta mika bukatarta ga shugabannin gargajiya, musamman wajen inganta lafiya mata
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Gombe - Masarautar Gombe ta jinjina wa Uwargidar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu bisa ayyukanta na taimakon talakan Najeriya.
A ranar 2 ga watan Oktoba, 2025, masarautar ta nada ta a matsayin Sarauniyar Yakin Akko dake Jihar Gombe, wato Sarauniyar da ke fafutukar kare hakkin marasa galihu.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta yi martani kan zargin jefa 'yan Najeriya miliyan 15 a bakin cikin talauci

Source: Facebook
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Lamidon Akko, Alhaji Umar Muhammad Atiku, ne ya ba da sarautar yayin da Uwargidar shugaban ƙasa ke ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin ba Remi Tinubu sarauta a Gombe
Punch ta ruwaito cewa Mai Martaba Sarkin ya ce an ba ta wannan sarauta ne a matsayin girmamawa ga kokarinta na kare muradun mata da yara.
Haka kuma wannan zai zo a matsayin godiya ta musamman a kan yadda ta ke kula da mutane marasa galihu a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Source: Facebook
Ta kuma sha alwashin ci gaba da jajircewa wajen samar da tallafi da tsare-tsare da za su inganta rayuwar yara mata da sauran masu rauni a cikin al'umma.
Remi Tinubu ta roki sarakuna
Sanata Remi Tinubu ta roki sarakunan gargajiya su bada goyon baya ga shirinta na wayar da kai da kuma ƙarfafa mata da yara mata ta fuskar ilimi da lafiya.
Wannan ziyara ta Uwargidar shugaban ƙasa ba ta tsaya kawai a sarauta ba, domin ana sa ran za ta kaddamar da wata sabon shiri ga mata.
Wannan shiri yana da nufin inganta lafiyar mata, musamman a lokutan al’ada da daliban da ke makarantun gaba da sakandare a fadin ƙasar.
Shirin na nufin tallafawa yara mata da kayan kula da jikinsu tare da wayar da kai kan tsafta da fahimtar jiki ta yadda za su rayu a cikin kwanciyar hankali.
Taron nadin sarautar ya samu halartar manyan jami'an gwamnati ciki har da Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya.
Sannan an ga Mai tsawatarwa a Majalisar Wakilai, Hon. Usman Bello Kumo, da wasu fitattun masu ruwa da tsaki a jihar.
An tara wa Remi Tinubu N20bn
A baya, mun wallafa cewa ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa, sun haɗa gudummawar Naira biliyan 20 domin girmama Uwargidar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu.
An tara mata kudin ne bayan ta bayyana cewa tana neman gudunmawar yadda za a sake gina babban dakin karatu na kasa a matsayin kyautar taya ta murnar zagayowar ranar haihuwarta.

Kara karanta wannan
Abuja ta zama abin tsaro, Tinubu ya ba da umarni bayan yi wa yar jarida kisan gilla
A cikin wani saƙon bidiyo da ta fitar, uwargidar shugaban ƙasar ta bayyana cewa ta yanke shawarar sadaukar da ranar haihuwarta, 21 ga Satumba, 2025 ga aikin dakin karatun.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
