Fargabar Ambaliya: Kainji da Manyan Madatsu 3 a Najeriya na Shirin Kwararo Ruwa

Fargabar Ambaliya: Kainji da Manyan Madatsu 3 a Najeriya na Shirin Kwararo Ruwa

  • Ana fargabar cewa manyan madatsun ruwa hudu a Neja za su iya kwararo ruwan mai yawan gaske da zai haifar da matsala
  • Hukumar NSEMA ta gargadi al’umman da ke bakin koguna su koma sama domin kaucewa ambaliyar ruwa mai hatsari
  • Gargadin ya zo ne yayin da aka ruwaito an riga an samu rugujewar gidaje, gonaki da hanyoyi a wasu kananan hukumomi na jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Neja - Gargadin cewa madatsun ruwa hudu na iya sakin ruwan da ya taru a cikinsu ya tayar da hankulan jama’a, musamman mazauna bakin koguna.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (NSEMA) ta bayyana cewa matakin na iya jawo mummunar ambaliya a wurare da dama.

Yadda ruwa ke gudana a madatsar Kainji
Yadda ruwa ke gudana a madatsar Kainji. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Vanguard ta wallafa cewa shugaban NSEMA Alhaji Abdullahi Arah, ya ce lamarin zai iya zama bala’i idan al’umman yankunan da abin ya shafa suka ci gaba da zama kusa da koguna.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun tilasta rufe makarantu 180 a Arewa

Hakan ya sanya hukumar ta shawarci jama’a da su yi gaggawar komawa wuraren da aka ware domin kaucewa hadarin.

Madatsun da za su kawo ruwa

Rahotanni sun nuna cewa ana fargabar ballewar ruwa ne daga madatsun Kainji, Jebba, Shiroro da Zungeru.

Hukumar NSEMA ta yi nuni da cewa ruwan da zai iya kwararowa daga madatsun na iya kawo ambaliya da ba za a iya shawo kanta ba.

Ta kuma gargadi jama’a da su guji gudanar da harkoki a bakin koguna yayin da ake fargabar kwararar ruwan.

Alhaji Arah ya kara da cewa hukumar NiMeT ta yi hasashen cewa ƙarshen daminar bana zai zo ne da iska mai karfi, wanda hakan zai iya kara ta’azzara matsalolin da jama’a ke fuskanta.

Illolin da aka riga aka gani a Neja

An ruwaito cewa wasu yankuna sun riga sun fara fuskantar illolin ambaliyar, inda gidaje da gonaki suka lalace tare da lalacewar gadoji da hanyoyin mota.

Kara karanta wannan

An lakadawa dan damfara duka bayan asirin shi ya tonu a tsakiyar kasuwar Neja

Kananan hukumomin da abin ya fi shafa sun hada da Lavun, Magama, Rafi, Kontagora, Gbako, Mokwa, Lapai da Katcha.

Haka kuma an tabbatar da asarar rayuka a wasu wurare, kodayake ba a bayyana adadin mutanen da suka mutu ba.

Jami'an NEMA yayin aika kayan agaji bayan ambaliya
Jami'an NEMA yayin aika kayan agaji bayan ambaliya. Hoto: NEMA Nigeria
Source: Getty Images

An gargadi al'umma kan ambaliya

Rahotanni sun nuna cewa wannan matsala ta shafi harkokin tattalin arzikin jama’a, musamman manoma da ’yan kasuwa a yankunan karkara.

PM News ta rahoto cewa NSEMA ta ce hakan na iya janyo karuwar matsalolin rayuwa ga al’umma a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a kasa baki daya.

Hukumar ta bukaci jama’a da su dauki wannan gargadi da muhimmanci, tare da bin hanyoyin tsira da aka tanada domin rage radadin da ka iya biyo baya.

NIMET ta ce za a yi ruwa da iska

A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar NiMet ta yi gargadi da cewa ana iya fuskantar ruwan sama mai yawan gaske a wasu jihohin Najeriya.

Hukumar hasashen yanayin ta bayyana cewa za a sha ruwan ne a jihohi da dama da suka hada da Gombe da Kano.

Kara karanta wannan

An shigar da 'yan sanda kotu, za a fara shari'a kan takaita hawa babur a Gombe

Domin ganin jama'a sun kubuta, hukumar NiMet ta fitar da gargadi tare da bayyana matakan da ya kamata mutane su dauka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng