Isra'ila za Ta Ji Haushi, Najeriya Ta Saki Shugaban Falasdinawa bayan Kama Shi
- Shugaban al’ummar Falasdinawa a Najeriya, Ramzy Abu Ibrahim ya samu ‘yanci bayan tsare shi da aka yi tun watan Agusta
- Tsohon minista, Femi Fani-Kayode ya tabbatar da sakin nasa a ranar 2, Oktoba, 2025, inda ya ce ya ziyarce shi a gidansa
- Kama shi ya janyo martani daga kungiyoyin kare hakkin Bil’adama da na addini da suka nemi a sake shi ba tare da sharadi ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – An saki Ramzy Abu Ibrahim, fitaccen jagoran al’ummar Falasdinawa da ke Najeriya, daga hannun jami’an tsaro bayan tsawon wata guda da ya shafe a tsare.
An ce jami’an sashen yaki da ta’addanci na ‘yan sanda ne suka kama shi a gidansa da ke Abuja a ranar 28, Agusta, 2025, abin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a kasar.

Kara karanta wannan
Da kusan mutane miliyan 100, Najeriya ta zama kasa ta 2 mafi yawan talakawa a Duniya

Source: Facebook
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ne ya tabbatar da sakin nasa a shafinsa na X a ranar 2, Oktoba, 2025, inda ya wallafa hotunansu tare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An saki shugaban Falasdinawan Najeriya
A cikin rubutunsa, Fani-Kayode ya bayyana farin cikinsa da ganin Abu Ibrahim a gidansa bayan sakin nasa, inda ya yabawa hukumomin tsaro kan yadda suka gudanar da bincike cikin basira.
Ya ce:
“Na gode wa hukumomin da suka nuna kwarewa da bin doka wajen tsare shi, kuma suka sake shi a lokacin da ya dace ba tare da tauye haƙƙinsa ba.”
Abu Ibrahim ya zama dan Najeriya
Ko da yake asalin dan Falasdinu ne, Abu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 30 a Najeriya, inda ya zama ɗan ƙasa.
Ya halarci Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), a nan ya samu digirinsa na farko, kuma yana iya magana da harsunan Hausa da Yarbanci sosai.
Fani-Kayode ya ce ya kasance shugaba mai kishin gaskiya da zaman lafiya, kuma ana ganinsa a matsayin murya mai kare hakkin Falasdinawa, musamman a kan rikicin Gaza.
Maganar da aka yi bayan kama shi
Kafin sakin nasa, kungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da na addini sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta sake shi nan take.
Legit Hausa ta rahoto cewa kungiyoyi da dama sun ce babu wata hujja da ta nuna cewa ya aikata laifi kafin a kama shi.
Rahoton Muslim News ya nuna cewa sakin nasa ya dawo da farin ciki da kwanciyar hankali a tsakanin Falasdinawa da ke Najeriya, da kuma abokan hulɗarsa na gida da waje.

Source: Facebook
Fadi-tashin Gaza da hare haren Isra'ila
Fani-Kayode ya bayyana cewa, duk da rashin da Abu Ibrahim ya yi, ciki har da rasa ‘yan uwansa sama da 33 a Gaza, bai daina magana kan mutanensa na Falasdinu ba.
Tsohon ministan ya kara da cewa jarumtakar Abu Ibrahim ta kara wa sauran masu fafutuka kwarin gwiwa wajen ci gaba da nuna goyon baya ga Falasdinawa.
Fani-Kayode yana cikin masu sukar abin da gwamnatin Benjamin Netanyahu ta ke yi.
Isra'ila ta hana kai agaji Gaza
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Isra'ila ta kai farmaki kan jiragen ruwan da suka nufi kai kayan agaji Gaza.
Rahotanni sun nuna cewa Yahudawan sun kama mutanen da suka taho daga kasashen duniya a cikin jiragen ruwan.
'Yan fafutuka masu rajin kare hakkin dan Adam ne suka shiga jiragen ruwa domin kai tallafi ga Falasdinawa bayan hare haren Isra'ila a Gaza.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

