Da kusan Mutane Miliyan 100, Najeriya Ta Zama Kasa Ta 2 Mafi Yawan Talakawa a Duniya

Da kusan Mutane Miliyan 100, Najeriya Ta Zama Kasa Ta 2 Mafi Yawan Talakawa a Duniya

  • Najeriya ta zama kasa ta biyu bayan kasar India da ke da yawan mutane masu rayuwa a cikin talauci a duniya
  • Tsohon Shugaban NBS, Yemi Kale ne ya bayyana haka a wurin wani taro da aka shirya ranar cikar Najeriya shekara 65 da samun yancin kai
  • A cewarsa, kamata ya yi a ce Najeriya ta wuce matakin da take a yanzu tun shekaru 10 da suka wuce

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon shugaban Hukummar Kididdiga Ta Kasa (NBS), Yemi Kale, ya ce kimaninn mutane miliyan 89, kashi 40 na al’ummar Najeriya, na rayuwa ne ƙasa da layin talauci.

Mista Kale ya bayyana haka ne a wajen taron The Platform Nigeria na bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, wanda aka gudanar a Legas.

Kara karanta wannan

"Ku daina": Tinubu ya yi nasiha ga 'yan Najeriya kan wata mummunar dabi'a

Tsohon Shugaban Hukumar NBS, Yemi Kale.
Hoton tsohon shugaban Hukumar NBS, Yemi Kale yayin gabatar da wata lakca a jihar Legas. Hoto: @sgyemikale
Source: Twitter

Masanin tattalin arzikin ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu mafi yawan talakawa a duniya bayan kasar Indiya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya ce ta 2 a yawan talakawa a duniya

Yemi Kale, wanda yanzu shi ne babban manazarcin tattalin arziki kuma Maanajan Darakta a Afreximbank, ya ce:

“Bari na fahimtar da ku girman wannan adadi, ƙasashen kimanin 20 daga cikin ƙasashen duniya 195 ne kawai ke da yawan jama’a da ya fi adadin talakawan Najeriya,” in ji shi.

Ya ce halin da ake ciki na talauci na ƙara ta’azzara kuma yana barazana ga alkawarin ’yancin kai da ya kamata kowanne ɗan Najeriya ya samu damar yin rayuwa mai inganci a ƙasarsa.

Me ya jawo karuwar talauci a Najeriya?

Kale ya ce dalilan da suka haifar da wannan matsala sun haɗa da kura-kuran da aka tafka a baya da kuma jinkirin aiwatar da gyare-gyaren da ake bukata.

Kara karanta wannan

Flotilla: Isra'ila ta kai hari kan masu kai agaji Gaza, wasu jiragen ruwa sun kubuta

"Sai yanzu ne aka fara wasu daga cikin tsare-tsaren da ya kamata a yi domin ceto kasar nan, tun sama da shekaru 10 da suka wuce ya kamata a ce mun wuce nan.
"Da mun fara da wuri, za a samu saukin wadannan wahalhalu da mutane da yan kasuwa suka shiga, kuma za mu ceci tattalin arzikin kasarmu daga hauhawar farashi.

- Yemi Kale.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Hoton Shugaban Kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a ofishinsa da ke Aso Rock. Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Tsohon Shugaban NBS ya kawo mafita

Tsohon shugaban NBC ya soki tsarin canjin kudin Najeriya na baya, yana mai cewa shi ne ya ruguza kwarin gwiwar masu zuba jari.

Mista Kale ya jaddada cewa gyare-gyaren da aka gabatar kwanan nan karkashin gwamnati mai ci suna da matukar wahala da radadi, amma “ba mu da wani zabi."

Tsohon shugaban NBS ya ce idan aka gudanar da gyare-gyaren da gaskiya da tsari, Najeriya za ta dauko hanyar kawar da talauci a tsakanin jama'arta.

"Wahala ta kare a Najeriya" - Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa lokacin wahala da matsin rayuwa ya wuce a Najeriya.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Jonathan ya aika da muhimmin sako ga 'yan Najeriya

A jawabinsa na ranar bikin samun yancin Najeriya, Tinubu ya tabbatarwa yan Najeriya za su fara shan romon manufofin gwamnatinsa.

Tinubu ya yi godiya ga 'yan Najeriya bisa juriya, fahimta da goyon baya, inda ya ce wahalhalun da aka sha a baya na shirin zama tarihi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262