"Ku Daina": Tinubu Ya Yi Nasiha ga 'Yan Najeriya kan Wata Mummunar Dabi'a
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da muhimmin sako ga 'yan Najeriya mazauna cikin gida da kasashen waje
- Mai girma Tinubu ya bukaci a rika tausasa harshe idan za a yi maganganu kan Najeriya domin hakan yana da muhimmanci
- Shugaban kasan ya nuna cewa Najeriya kasa ce ta mutane masu daraja da bai kamata a rika munanan kalamai a kanta ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi muhimmin kira ga ‘yan Najeriya da ke zaune a cikin gida da kasashen waje.
Shugaba Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya da su daina yin magana cikin mummunan salo kan kasar, yana mai jaddada cewa Najeriya kasa ce mai daraja da kuma dimbin albarkatu.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wajen kaddamar da cibiyar al'adu ta Wole Soyinka da aka gyara, a Legas ranar Talata, 30 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan
Gwamna ya lallaba ya gana da Tinubu, za a saki jagoran 'yan ta'adda da Buhari ya kama a 2021
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara Tinubu ya ba 'yan Najeriya?
Shugaba Tinubu ya jaddada bukatar ‘yan kasa su yi imani da Najeriya tare da yin aiki tukuru wajen ci gabanta.
“Ina so na yi amfani da wannan dama na faɗi abu ɗaya mai matuƙar muhimmanci a wurina, a wurinku da kuma ga gwamnatina. Ku daina magana game da Najeriya da mummunan salo."
"Wannan kasa ce ta mutane masu kima, kasa ce ta jarumai, mutane masu kwarin gwiwa da sadaukarwa. Mu hadu tare mu gina ta. Mu sake kirkirarta."
- Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Tinubu ya kuma yi amfani da wannan damar wajen tunawa da irin fasaha da al’adun Najeriya, inda ya bayyana cewa ɗimbin baiwar da kasar ke da ita, na ɗaya daga cikin babban arzikin da take da shi.
Ya yabawa fitaccen marubuci, Farfesa Wole Soyinka, wanda ya bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin kwararrun masana masu kirkira, bisa rawar da ya taka wajen ci gaban kasa da kuma fannin adabi.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta yi martani kan zargin jefa 'yan Najeriya miliyan 15 a bakin cikin talauci
Tinubu ya tuna baya kan cibiyar al'adu
Tinubu ya kuma waiwayi tarihin cibiyar al'adu ta kasa, inda ya bayyana sabunta wajen a matsayin alamar juriya da kwazon Najeriya, labarin ya zo a tashar Channels.

Source: Facebook
"Wannan wuri ba zai sake lalacewa, ya zama tarkace ba. Bai kamata mu rasa wannan dama ba wajen kirkirar ayyukan yi, da inganta kula da muhalli, da wayar da kai da kuma ɗa’a."
- Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Tinubu ya jinjinawa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyon bayansu.
Hakazalika, ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaban tattalin arzikin kasa.
Masa'udu Mika ya shaidawa Legit Hausa cewa tabbas bai kamata 'yan kasa na yin kalamai marasa kyau ga kasarsu ba.
Amma ya nuna cewa wasu lokutan shugabanni ne suke kure mutane ta hanyar yin rikon sakainar kashi da bukatun jama'a.
"Tabbas kasa abin girmamawa ce wadda za a yi alfahari da ita. Bai kamata a rika kalaman bata sunanta ba."
"Amma a wasu lokutan shugabanni ne suke jawo hakan kan yadda suke gudanar da jagorancinsu."
- Masa'udu Mika
Akpabio ya yi wa Tinubu albishir kan 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samu albishir daga wajen shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Sanata Godswill Akpabio ya sanar da Shugaba Tinubu cewa wasu gwamnonin jam'iyyun adawa za su dawo jam'iyyar APC.
Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa tuni gwamnonin suka kammala shirin dawowa jam'iyya mai mulki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
