Kurunkus: Kotu Ta Yanke Hukunci kan Ingancin Dokar Ta Bacin da Tinubu Ya Sa a Ribas
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a karar da aka kalubalanci dokar ta-bacin da ya ayyana a jihar Ribas tun watan Maris, 2025
- Babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta yi fatali da kasar, tana mai cewa masu kara sun gaza habatar da hujja fiye da ta gwamnatin tarayya
- Alkalin Kotun na Tarayya ya ce masu karar ba su da hurumin kalubalantar matakin, kuma kotun koli ce ke kadai ke da ikon sauraron batun
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babbar Kotun Tarayya Mai Zama a Abuja ta yi fatali da karar da aka shigar ta kalubalantar dokar ta-bacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sa a jihar Ribas.
Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke wannan hukunci, inda ya yi watsi da karar da aka shigar kan ayyana dokar ta-baci da Tinubu ya yi a Jihar Ribas a ranar 18 ga Maris, 2025.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta yi martani kan zargin jefa 'yan Najeriya miliyan 15 a bakin cikin talauci

Source: Twitter
Matakan da Bola Tinubu ya dauka a Ribas
Leadership ta tattaro cewa bayan ayyana dokar ta baci, Tinubu ya kuma dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da ’yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sannan kuma shugaban kasa ya nada shugaban riko domin kula da harkokin jihar Ribas na tsawon wannan lokacin.
Sakamakon rashin gamsuwa da wannan mataki, Belema Briggs da wasu mutum huɗu suka kalubalanci Tinubu a kotu, inda suka yi zargin cewa wannan mataki ya tauye musu ’yancinsu.
Hukuncin da Kotun Abuja ta yanke
A hukuncin da ya yanke yau Alhamis, Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa masu shigar da karar ba su da hurumin doka da zai ba su damar shigar da kara a gaban kotu.
Bugu da kari, alkalin ya bayyana cewa kotun koli ce kaɗai ke da ikon yanke hukunci kan irin wannan batu.
Mai shari’ar ya kara da cewa masu karar sun gaza kawo shaidar cewa suna daga cikin yan Majalisar Dokokin Ribas ko mambobin Majalisar Zartarwa ta jiha (SEC).

Kara karanta wannan
"Mun ceto Naira," Tinubu ya tabo batun darajar kudin Najeriya a jawabin ranar 'yanci
A cewar alkalin, hakan ya sa masu karar suka gaza gamsar da kotu cewa matakin ayyana dokar ta-bacin ya cutar da su fiye da yadda ya cutar da jama'ar Ribas.
Abubuwan da kotu ta gano a shari'ar
Hukuncin da kotun ta yanke ya nuna cewa masu karar sun shigar da korafi gaban kotu ba tare da amincewar Antoni Janar na jihar Ribas kuma kwamishinan shari'a ba.
Mai shari’a Omotosho ya ce babu wanda ya iya kawo hujjar da ta take hujjar Shugaba Tinubu cewa ya ayyana dokar ta-bacin ne domin dakile tashin rikici da barazana ga tsaro.

Source: Twitter
Ya kammala da cewa karar “ba ta da tushe kuma ba ta da amfani” domin masu shigar da ita ba su da goyon bayan jama’ar Jihar Ribas, wannan ya sa ya kori karar gabata daya.
Shugaba Tinubu ya gana da gwamnan Ribas
A wani labarin, kum ji cewa Gwamna Simi Fubara na jihar Ribas ya lai ziyara fadar shugaban kasa awani kadan bayan Tinubu ya maida shi kan mulki.
Gwamnan ya samu ganawa da Shugaba Bola Tinubu ya sirrance, inda ake kyautata zaton sun tattauna ne kan batutuwan da suka shafi Ribas.
Fadar Shugaban Kasa da Gwamna Fubara ba su bayyana ainihin abin da shugabannin biyu suka tattauna a hukumance ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
