Tinubu Ya Yi Kira ga 'Yan Najeriya a Taron da Ya Hadu da Sanusi II a Legas

Tinubu Ya Yi Kira ga 'Yan Najeriya a Taron da Ya Hadu da Sanusi II a Legas

  • Rahotanni sun bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ba za ta ruguje ba a lokacin shugabancinsa
  • Shugaban ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da cibiyar al'adu ta Wole Soyinka da aka yi wa gyara a jihar Legas
  • Khalifa Muhammadu Sanusi II na cikin manyan Najeriya da suka raka shugaban kasa wajen kaddamar da cibiyar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya za ta ci gaba da kasancewa ƙasa mai ƙarfi, ba tare da ta ruguje a lokacin shugabancinsa ba.

Ya yi wannan bayani ne yayin ƙaddamar da cibiyar raya al'adu ta Wole Soyinka da aka sabunta a garin Legas.

Shugaba Tinubu tare da Khalifa Sanusi II
Shugaba Tinubu tare da Khalifa Sanusi II. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A wani sako da ta wallafa a shafinta na X, Masarautar Kano ta bayyana cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya hallara wajen.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu ya fada a jawabin ranar samun 'yanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sake wa cibiyar suna suna ne a watan Yulin 2024 domin girmama fitaccen marubuci, Farfesa Wole Soyinka.

'Najeriya ba za ta rushe ba' - Tinubu

Yayin jawabinsa, Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta riga ta wuce mafi muni a cikin matsalolin tattalin arziki.

Shugaban kasar ya bayyana cewa yana da yakinin cewa ci gaba da wadata za su dawo cikin ƙasar a nan gaba.

“Na faɗa jiya kuma zan maimaita yau, mun bar yanayi mafi muni a baya. Tattalin arziki ya murmure, kuma na tabbata za mu cigaba."
"Wannan ƙasa ita ce jagora a Afirka, ba za ta rushe ba, ba kuma za ta ruguje a hannuna ba,”

- In ji shi.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya a gida da ƙasashen waje da su daina magana da kalaman cin mutunci kan ƙasar.

Ya ce wajibi ne kowa ya ɗaga matsayin Najeriya ta hanyar alfahari da abin da aka gada daga iyaye da kakanni.

Kara karanta wannan

Tinubu ya cire kunya ya fadi abin da ya gaza yi a rayuwarsa a gaban 'yan APC

Sanusi II ya hadu da Tinubu a taron

A wajen taron, Tinubu ya samu rakiyar uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu, gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio.

Mataimakin shugaban majalisa Barau Jibrin, shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas, mataimakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, da Sarki Sanusi II sun halarci taron.

Shi kansa Farfesa Wole Soyinka ya halarci taron a matsayin bako na musamman, inda Tinubu ya bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan duniya da suka bayar da gudummawa sosai.

Tinubu tare da Wole Soyinka yayin kaddamar da cibiyar
Tinubu tare da Wole Soyinka yayin kaddamar da cibiyar. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Bayanin gwamnan CBN a taron

Daily Trust ta wallafa cewa gwamnan Babban Bankin Najeriya, Yemi Cardoso, ya bayyana cewa sabunta cibiyar aiki ne na raya harkokin al’adu da fasaha a Najeriya.

Ya ce cibiyar ta samu sababbin dakunan wasan kwaikwayo na zamani, ɗakunan baje koli, ɗakin karatu na adabin Afirka, dakunan atisaye, sinima, da kuma kayayyakin more rayuwa.

Cardoso ya ce an bar fasalin cibiyar yadda take tun farko, amma an ƙara mata ingantattun abubuwan zamani domin ta zama matattarar al’adu a Afirka.

Kara karanta wannan

Bayan wuya: Tinubu ya fadi yadda sauki ya fara samu wa Najeriya

Atiku Abubakar ya ragargaji Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki shugaban Bola Tinubu.

Atiku Abubakar ya yi magana ne yayin da Najeriya ta cika shekara 65 da samun yancin kai a ranar 1 ga Oktoban 2025.

Ya bayyana cewa matsalar tsaro ta yi katutu a Najeriya amma shugaba Tinubu bai nuna alamar damuwa da hakan ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng