Buhari da 'Yar'adua Sun Shiga Jerin Mutane Sama da 100 da Suka Yi Fice a Katsina
- Rahotanni sun bayyana cewa an ƙaddamar da wani littafi mai ɗauke da tarihin fiye da manyan mutane 100 daga jihar Katsina
- Tsofaffin shugabannin ƙasa, Umaru Musa Yar’Adua da Muhammadu Buhari, na cikin fitattun mutanen da aka jera a littafin
- Gwamna Dikko Radda da sauran masu ruwa da tsaki sun jaddada muhimmancin littafin wajen wa’azi ga matasa da raya tarihi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - An yi wani gagarumin bikin ƙaddamar da littafi da ke tattara tarihin fitattun mutanen Katsina da suka taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasa.
Littafin da aka wallafa ƙarƙashin taken 100+ Eminent Nigerians from the Katsina State: Profiles in Nation Building and History ya kunshi bayanai kan sama da mutum 100 da suka fito daga jihar.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook cewa Dikko Radda ya hallara taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsofaffin shugabannin ƙasa biyu daga jihar, marigayi Umaru Musa Yar’Adua da marigayi Muhammadu Buhari, na daga cikin waɗanda aka lissafa a littafin.
An gabatar da littafin a babban taro da aka gudanar a Katsina ranar Laraba, wanda ya samu halartar jami’an gwamnati da masana.
Jawabin gwamnan Katsina, Dikko Radda
A yayin jawabi, Gwamna Dikko Umar Radda ya bayyana cewa ba wai domin tarihi kawai aka ƙaddamar da littafin ba, har ila yau ya kunshi ba matasa damar samun abin koyi.
Ya ce littafin zai taimaka wajen nuna irin gudummawar da mutanen Katsina suka bayar a fannoni daban-daban na ci gaban ƙasa.
Ya yi kira ga iyaye da makarantu da su yi amfani da littafin wajen koyar da yara darusa, domin su san irin sadaukarwar da wasu mutanen jihar suka yi don al’umma.
Bayanin masu ruwa da tsaki
Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba-Faskari, ya bayyana littafin a matsayin muhimmiyar hujja mai cike da tarihi da zaburarwa ga matasa.
Ya ce kasancewar an lissafa fitattun mutane sama da 100 ya sa littafin ya zama ginshiƙi wajen ilmantarwa da faɗakarwa.
Haka zalika, mai nazarin littafin, Dr Aliyu Rabiu-Kurfi, ya bayyana shi a matsayin abin tunawa na musamman ga jihar.
Ya ce yayin da jihar ta yi bikin cika shekara 38 da kafuwa, littafin ya zama hujja ta gudumawar al’ummarta ga ƙasar.

Source: Facebook
An karrama Buhari da 'Yar'adua
Littafin ya tuna wa mutane da irin jagorancin da marigayi shugaba Umaru Musa Yar’Adua da Muhammadu Buhari suka yi.
Yar’Adua ya jagoranci Najeriya daga 2007 zuwa karshen rasuwarsa a watan Mayun 2010, inda ya kasance shugaban ƙasa na dimokuraɗiyya.
Muhammadu Buhari kuwa ya fara mulki a matsayin shugaban soja daga 1983 zuwa 1985, sannan ya sake komawa kan mulki a matsayin shugaban ƙasa daga 2015 har zuwa 2023.

Kara karanta wannan
'Yan Boko Haram sun yi ta'addanci a Borno, an kona fadar basarake, an kashe mutane
Tinubu ya ziyarci iyalan Buhari
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci iyalan marigayi Muhammadu Buhari.
Tinubu ya ziyarce su ne a karon farko bayan komawarsu Kaduna bayan kammala zaman makokin marigayin a gidansa na Daura a Katsina.
Shugaban kasar ya ziyarci jihar Kaduna ne domin halartar daurin auren dan Sanata Abdulaziz Yari a watan Satumban 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

