Sheikh Triumph: Guruntum Ya Magantu kan Zargin Batanci, Ya Yi Kira ga Gwamna Abba

Sheikh Triumph: Guruntum Ya Magantu kan Zargin Batanci, Ya Yi Kira ga Gwamna Abba

  • Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya bayyana ra’ayinsa game da zargin batanci kan Sheikh Lawal Abubakar Triumph
  • Ya ce bai kare Sheikh Triumph ba, sai dai ya nemi a tabbatar da gaskiyar lamarin yayin da majalisar shura ta Kano ke aikinta
  • Malam Guruntum ya bukaci gwamnati da al’umma su bar doka ta yi aikinta, sannan ya yi gargadi ga masu daukar doka a hannu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi – A yayin wani wa’azi da ya gabatar a garin Bauchi a ranar 01, Oktoba, 2025, Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya yi tsokaci kan zargin bataci da ake a Kano.

Sheikh Guruntum ya yi magana ne kan ge-zargen batanci da ake yi wa Sheikh Lawal Abubakar Triumph a Jihar Kano.

Kara karanta wannan

Haramun ne: Malamin Musulunci ya yi gargadi kan gwajin kwayar halitta ta DNA

Sheikh Gurunum yayin wani wa'azi.
Sheikh Gurunum yayin wani wa'azi. Hoto: Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai kan abin da Sheikh Guruntum ya fada ne a wani bidiyo da aka wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin laccar, Sheikh Guruntum ya ce ya yi magana ne domin bayyana gaskiya da kuma tantance hakikanin abin da ya ke faruwa ba goyon bayan wani ba.

Sheikh Guruntum ya ce gaskiya ya ke nema

Sheikh Guruntum ya jaddada cewa ba ya nufin kare Sheikh Triumph daga zargi, amma yana son a tabbatar da cewa abin da ake kiran batanci gaskiya ne kafin a yanke hukunci.

Ya ce wasu maganganun da ake yadawa basu da tabbaci, don haka dole a dawo kan tushen zancen yayin bincike.

Ya bayyana cewa:

"Idan ana so a hukunta shi, sai an tabbatar da abubuwan da ya fada ga Annabi, na yi imami idan sun tabbata sifofin Annabi ne, idan aka cewa malam Lawal ya fito tsirara ya tuba zai tuba."

Kara karanta wannan

Da sauran rina a kaba: Gwamna Abba ya yi maganar cikar Najeriya shekara 65 da 'yanci

Malamin ya kara da cewa:

"Yau idan da siffa ce ta Annabi ya soka, ridda ne."

Magana kan mafarki da siffar Annabi (SAW)

Sheikh Guruntum ya yi tsokaci kan maganar da wani malami ya yi game da ganin rakumi a mafarki da cewa zai iya yiwuwa Annabi (SAW) aka gani.

Guruntum ya ce ba daidai ba ne a ce wanda ya yi mafarki ya ke nuni cewa ya ga Annabi (SAW) kai tsaye.

“Duk duniya ba wanda ya isa ya rikida zuwa siffar Annabi (SAW).”

In ji shi, yana mai kalubalantar wadanda ke yada irin wannan maganganu da su yi taka-tsan-tsan.

Sheikh Lawal Triumph da ake zargi da batanci a Kano
Sheikh Lawal Triumph da ake zargi da batanci a Kano. Hoto: Sheikh Lawal Shuaibu Abubakar Triumph
Source: Facebook

Kiran Sheikh Guruntum ga gwamnatin Kano

Sheikh Guruntum ya yi Allah-wadai da kalaman da mataimakin gwamnan Kano ya yi na cewa akwai siyasa a cikin kama Sheikh Abduljabbar.

Malamin ya yi magana yana mai cewa irin wannan furuci bai dace ba a lokacin da ake fargabar tashin hankali a jiharsa.

Ya kuma bukaci mutane su kwantar da hankali, su bar doka ta yi aikinta, sannan kada kowa ya dauki doka a hannunsa.

Kara karanta wannan

Batanci: Malaman Izala sun yi zama kan maganar 'sakin' Abduljabbar Nasiru Kabara

Ya gargadi wadanda ke cewa za su kashe Sheikh Triumph da cewa daukar doka a hannu zai jefa su cikin nadama.

Kiran da Sheikh Khalil ya yi a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban malaman jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya yi magana kan zargin batanci da aka yi.

Malamin ya bayyana cewa mukabala da malamai ba za ta kawo mafita ga matsalar ba domin kowa na kokarin kare kan shi ne.

Ya bukaci a zauna da malamai domin su fahimci juna su daina yin maganganun da za su tunzura al'umma ko kawo rikici a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng