Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwa a Najeriya, an Yi Asarar Miliyoyin Naira
- Mummunar gobara ta lakume dukiyar miliyoyin Naira a kasuwar Bariga da ke jihar Legas a safiyar ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025
- Hukumar LASEMA ta sanar da cewa, gobarar ta fara ne daga shago daya, sannan sai ta fadada zuwa sauran shagunan kasuwar
- Jihar Legas ta fuskanci mummar tashin gobara har sau biyu a kwana kwanan nan, da suka jawo asarar rayuka da tarin dukiya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - 'Yan kasuwa da dama sun kirga asara bayan da mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar Bariga da ke jihar Legas.
An ce gobarar ta lakume akalla shaguna 26, lamarin da ya jawo asarar miliyoyin Naira a safiyar ranar Laraba.

Source: Twitter
Gobara ta tashi a kasuwar Legas
Gobarar na zuwa awanni 24 bayan hukumar LASEMA ta yi wani taro na masu ruwa da tsaki kan kiyaye hadurra a jihar, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar ta rahoto cewa shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce gobarar ta tashi da karfe 4:00 na safe.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Olufemi Oke-Osanyintolu ya ce ko kafin jami'ai su isa waje, tunu gobarar ta lakume wasu shaguna.
Olufemi Oke-Osanyintolu, ya kara da ce:
"Bayanan da muka tattara sun nuna cewa wutar ta tashi ne daga wani shago, sai ta ci gaba da ci tana yaduwa a sauran shagunan."
An yi asarar dukiyar miliyoyin Naira a gobarar
Shugaban LASEMA ya ci gaba da cewa:
"Babbar matsalar da aka samu ita ce, mafi yawan shagunan an gina su ne da katakai, don haka ne ya sa wutar ta yi barna sosai.
"An samu nasarar kashe gobarar ne ta hadin gwiwar hukumomin ba da agajin gaggawa, kuma an dakile wutar daga mamaye sauran shagunan kasuwar.
"Hakazalika, mun killace yankin da gobarar ta tashi domin hana bata gari satar dukiyar jama'a, ko kuma faruwar wani abu mai muni."
Shugaban ya ce har zuwa lokacin fitar da sanarwar, ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba, amma shaguna 26 suka kone, kuma an yi asarar miliyoyin Naira.

Source: Twitter
Legas tana fuskantar tashin gobara
Jaridar Punch ta rahoto cewa ko a ranar 18 ga Satumba, 2025, mutane bakwai aka tabbatar sun mutu bayan wata gobara da ta tashi a ginin Afriland da ke Legas.
An ce mutanen bakwai sun mutu a asibitoci daban daban, lokacin da aka hanzarta da su can don samun kular gaggawa bayan tashin gobarar.
Wannan lamari ne na daga cikin gobara biyu masu muni da aka samu a Legas a baya bayan nan, inda aka tafka asarar dukiya mai yawa, kuma aka rasa rayuka.
Mummunar gobara ta tashi a kasuwar Sokoto
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan kasuwa sun shiga halin jimami bayan mummunar gobara ta jawo musu asarar dukiya mai yawa a Sokoto.
Mummunar gobarar wacce ta tashi a fitacciyar kasuwar Kara da ke Sokoto ta lalata shaguna masu yawa da jawo asarar dukiyar miliyoyin naira.
Jami'an hukumomin ba da agaji na SEMA da NEMA sun ziyarci kasuwar tare da ba da tabbacin tallafi ga mutanen da gobarar ta jawo musu asara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

