Gwamna Fintiri Ya Yi Afuwa ga Masu Laifi don Murnar Cikar Najeriya Shekara 65 da Samun 'Yanci
- Gwamnan jihar Neja, Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi afuwa ga wasu daga cikin fursunonin da aka daure a gidajen gyaran hali
- Ahmadu Fintiri ya yi afuwar ne don murnar bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya
- Gwamnan ya bayyana cewa ya yi musu afuwar ne bayan an ga babban canji a cikin dabi'unsu da halayensu a zaman da suke yi a gidajen gyaran hali
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya yi afuwa ga fursunoni shida da ke zama a gidan gyaran hali.
Gwamna Fintiri ya yi afuwar ne ga fursunonin wadanda aka yankewa hukuncin zaman gidan kaso daban-daban a wasu cibiyoyin gyaran hali na jihar.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta rahoto cewa tafiyar ta zo ne a cikin bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai na Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya na murnar cika shekara 65 da 'yancin kai
Ana gudanar da bikin ranar samun ‘yancin kai a Najeriya a duk shekara a ranar 1 ga watan Oktoba.
Hakazalika ana bada hutu domin tunawa da ‘yantar da kasar daga mulkin mallakar Birtaniya a shekarar 1960.
Ana gudanar da wannan biki a faɗin kasa da jawabin shugaban kasa, tarurrukan gwamnati, bukukuwa, yayin da makarantu da gwamnatocin jihohi kan shirya shirye-shirye na musamman don girmama wannan rana.
Sai dai a bana, gwamnatin tarayya ta soke al’adar gudanar da faretin sojoji da aka saba yi a ranar bikin murnar samun 'yancin kai.
Meyasa gwamna Fintiri ya yi wa fursunoni afuwa?
The Guardian ta ce a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 1 ga watan Oktoban 2025, Gwamna Fintiri ya bayyana cewa fursunonin sun nuna babban canji a halayensu da ɗabi’unsu.
"Saboda haka, a cikin aiwatar da hakkin yin afuwa da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada, tare da bin shawarar kwamitin jihar Adamawa mai ba da shawara kan hakkokin afuwa."
"Na yafewa mutane shida da suka shafe wasu shekaru a gidan yari, waɗanda suka nuna hali mai nagarta a tsawon lokaci."
- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri

Source: Twitter
Gwamnan ya umarci a saki fursunonin nan take, tare da bada umarni ga hukumomin da abin ya shafa da su aiwatar da umarnin ba tare da jinkiri ba.
Waɗanda aka saki sun haɗa da: Wamari Godwin, Abraham Marksunil, David Paul, Ibrahim Adamu, Usman Inuwa, da Sani Yahaya.
Karanta wasu labaran kan jihar Adamawa
- Majalisa ta kara wa gwamna karfi, ta sauya dokar nadawa da sauke Sarki daga mulki
- Sabuwar cuta mai cin naman jiki ta bulla a Adamawa, gwamnati ta fara bincike
- Ambaliya ta mamaye Adamawa, an gargadi Sokoto da wasu jihohi 12
'Yancin kai: Sakon Jonathan ga 'yan Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya taya 'yan Najeriya murnar cika shekara 65 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka.
Goodluck Jonathan ya bukaci 'yan Najeriya da su ci gaba sanya kishin kasa a cikin dukkanin ayyukan da za su gudanar.
Tsohon shugaban kasa ya kuma bukaci 'yan Najeriya su ci gaba da jajircewa wajen hada kawunansu don ganin kasar ta kai inda ake so.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


