Nigeria @65: Muhimman Abubuwa 5 da Tinubu Ya Fada a Jawabin Ranar Samun 'Yanci

Nigeria @65: Muhimman Abubuwa 5 da Tinubu Ya Fada a Jawabin Ranar Samun 'Yanci

A yau Laraba, 1 ga Oktoban 2025, shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi bayanin ranar 'yancin kai na kasar bayan cika shekara 65.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja A cikin jawabinsa na cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yancin kai a ranar Laraba, Bola Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa kasar na kan turba.

Tinubu ya roƙi ’yan ƙasa da su ci gaba da hakuri, yana mai jaddada cewa mummunan yanayi ya wuce, alheri kuma na kusa.

Shugaban Najeriya, yana wani jawabi
Shugaban Najeriya, yana wani jawabi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun kawo muku wasu muhimman abubuwa biyar (5) da shugaban kasar ya fada a bayanin da ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Ci gaban tattalin arziki

Tinubu ya bayyana cewa GDP na Najeriya ya karu da kashi 4.23 a zango na biyu na shekarar 2025, yayin da hauhawar farashin kaya ta sauka zuwa kashi 20.12.

Kara karanta wannan

"Ku daina": Tinubu ya yi nasiha ga 'yan Najeriya kan wata mummunar dabi'a

Ya danganta wannan ci gaba da tsauraran matakan gyara da suka haɗa da cire tallafin mai da daidaita farashin musayar kuɗi.

Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa Tinubu ya ce:

“Cikin shekaru biyu na mulkinmu, mun cimma manyan nasarori guda 12 a fannin tattalin arziki sakamakon aiwatar da ingantattun manufofin kuɗi da na kuɗin shiga.”

2. Magana kan asusun kudin wajen Najeriya

Ya ce kudin asusun ajiyar wajen Najeriya ta ƙaru zuwa Dala biliyan 42.03, mafi girma tun shekarar 2019, kuma Najeriya tana samun riba a cinikayyar waje sosai.

Wannan, a cewar shugaba Tinubu, shaida ce ta ƙaruwar amincewar masu zuba jari da tattalin arzikin ƙasar.

3. Maganar biyan bashin Najeriya

Tinubu ya ce kudin da ake amfani da shi wajen biyan bashi daga cikin kuɗin shiga ya ragu daga kashi 97 cikin 100 a 2022 zuwa ƙasa da kashi 50 a halin yanzu.

Ya bayyana cewa hakan ya ba da sarari ga gwamnati wajen saka hannun jari a fannin lafiya, ilimi, gina ababen more rayuwa da kuma walwalar jama’a.

Kara karanta wannan

Gwamna Fintiri ya yi afuwa ga masu laifi don murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun 'yanci

4. Samar da man fetur da makamashi

Shugaban ya sanar da an kara adadin man fetur da ake hakowa, inda ya ce ana samar da danyen mai da ya kai ganga miliyan 1.68 a rana.

Ya ce ya yi murna da dawo tace man fetur a cikin gida bayan kusan shekaru 40, yana mai cewa wannan zai ƙara ƙarfin tsaron makamashi da rage dogaro da kasar waje

Sugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Sugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

5. Tinubu ya ce an yi ayyuka

Tinubu ya bayyana cewa manyan ayyuka kamar hanyar bakin teku ta Lagos–Calabar da layin dogo na Kano–Maradi suna ci gaba da tafiya.

Punch ta ce shugaban ya bayyana su a matsayin zuba jari na sauyi da za su ƙarfafa cinikayya, samar da ayyukan yi da kuma ƙara haɗin kai a ƙasar.

Legit ta tattauna da Hajiya Maryam

Wata Hajiya a Abuja, Maryam Ahmad ta zantawa Legit cewa ta gamsu da yadda Bola Tinubu ke tafiyar da mulki a Najeriya.

Ta ce:

Kara karanta wannan

Jerin tsofaffin gwamnonin Najeriya 7 da suka dawo manyan sarakuna

"Na gamsu da yadda ya ke tafiyar da mulki. Kuma lallai zan kara zaben shi a karo na biyu.
"Duk wanda nake da iko a kan shi zan sa ya zabe shi, kaima ina kiranka da ka zabe shi."

Atiku ya caccaki Tinubu a ranar 'yanci

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan ranar 'yancin Najeriya.

Atiku ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan rashin tsaro da ake fama da shi a yankuna da dama na kasar.

Ya bukaci 'yan Najeriya su yanki katin zabe domin kayar da gwamnatin APC da ya ce ta gaza kare rayukan 'yan kasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng