Tinubu Ya Cire Kunya Ya Fadi Abin da Ya Gaza Yi a Rayuwarsa a gaban 'Yan APC
- Shugabam Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya sha ƙoƙarin cimma wani abu a rayuwarsa amma har yanzu bai samu dama ba
- Ya yaba wa Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo saboda rubuta littafi kan nasarorin da jam'iyyar APC ta samu a shekara 10 da suka wuce
- Bola Tinubu ya ce jam'iyyar APC ta kawo gagarumin sauyi kuma Najeriya ta tsallake mawuyacin lokaci cikin shekaru 10 da suka wuce
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Imo – A ranar 30, Satumba, 2025, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kokarin rubuta littafi da ya yi a baya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a Owerri, jihar Imo, yayin taron kaddamar da littafin da Gwamna Hope Uzodimma ya rubuta mai suna “A Decade of Impactful Progressive Governance in Nigeria”.

Source: Twitter
Premiuim Times ta wallafa cewa shugaba Bola Tinubu ya ce rubuta littafi abu ne mai matuƙar wahala.
Bola Tinubu ya gaza rubuta littafi
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya yi ƙoƙarin rubuta littafi sau da dama, amma haƙar shi bata cimma ruwa ba.
Ya bayyana cewa wallafa littafin Uzodimma dama ce ta tunawa da gwagwarmaya da sadaukarwa da aka yi wajen gina jam’iyyar APC da kuma ci gaban Najeriya.
Tinubu ya yabi littafin Uzodimma
Shugaba Tinubu ya yaba da kokarin Gwamna Hope Uzodimma, inda ya kira shi da mutum mai hangen nesa da kishin ƙasa.
Ya ce rubuta tarihin nasarorin APC cikin shekaru 10 wata kyauta ce ga Najeriya, domin babu wata ƙasa da za ta manta da hakan.
“Wannan littafi ya tabbatar da ci gaba da nasarorin da aka samu, kuma ya nuna yadda jam’iyyar APC ta shawo kan kalubale da dama tun bayan kafuwarta,”
In ji Tinubu yayin da mahalarta taron suka tafa hannu da nuna jin daɗi.
APC ta kawo sauyi inji Tinubu
Shugaban na Najeriya ya ce cikin shekaru 10 da APC ta jagoranci ƙasar, an samu sauye-sauye masu muhimmanci.
Ya bayyana cewa wadanda suka yi mulki a baya sun kusa ruguza ƙasar, amma gwamnatin APC ta dakatar da wannan matsala.
Ya ce:
“Mun yi alkawarin kawo sauyi, kuma yanzu zan iya cewa lokacin wahala ya wuce,”
Dalilin rubuta littafin Uzodimma
A nasa jawabin, Gwamna Hope Uzodimma ya bayyana cewa abin da ya sa ya rubuta littafin shi ne sha’awarsa ta rubuta tarihin nasarorin jam’iyyar APC ba tare da ɓoye gaskiya ba.
Ya ce littafin ya ba da cikakken labarin yadda APC ta kafa kanta daga ƙungiyar jam’iyyu ƙanana zuwa babbar jam’iyya mai mulki a Najeriya.
Punch ta wallafa cewa manyan 'yan siyasa ciki har da gwamnoni ne suka hallara wajen kaddamar da littafin.

Source: Facebook
Shugaba Tinubu ya yi bayanin ranar 'yanci
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi bayanin ranar 'yanci ga 'yan kasa.

Kara karanta wannan
Taron tsintsiya: Fadar Shugaban Kasa ta fadi kallon da Tinubu ke yi wa 'yan hadaka
Shugaban kasar ya ce duk da kalubale da aka fuskanta kasar tana kan hanyar murmurewa daga matsalar tattali da ta shiga a baya.
Ya kara da cewa an yi amfani da kudin tallafin man fetur da aka cire wajen ayyukan raya kasa domin inganta rayuwar jama'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

